Hotuna: Sojin Sun Ragargaji 'Yan Bindiga Har Maboyarsa, Sun Ceto Mutum 10

Hotuna: Sojin Sun Ragargaji 'Yan Bindiga Har Maboyarsa, Sun Ceto Mutum 10

  • Rundunar sojin Najeriya sun ragargaza wasu 'yan bindiga masu yawa da samamen da suka kai tsaunikan Apewohe, Dakwala da Kunai
  • Kamar yadda Samuel Aruwan ya bayyana, dakarun sun je kakkabar daji inda suka ceto mutum 10 daure da kaca
  • Sojojin sun kakkabe wani sansanin 'yan ta'addan dake Daban Lawal Kwalba a karamar hukumar Igabi

Kaduna - Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Forest Sanity sun halaka 'yan bindiga masu tarin yawa tare da ceto wasu mutum 10 daure da kaca a samamen da suka kai maboyar masu garkuwa da mutane a kananan hukumomijn Chikun da Igabi a jihar Kaduna.

Kamar yadda kwamishinan lamurran cikin gida, Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na Twitter, dakarun sun kai samamen sansanonin 'yan ta'addan dake tsaunikan Apewohe, Dakwala da Kunai a karamar hukumar Chikun.

Bandits and Soldiers
Hotuna: Sojin Sun Ragargaji 'Yan Bindiga Har Maboyarsa, Sun Ceto Mutum 10. Hoto daga @samuelaruwan
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A takardar da ya fitar a ranar Talata, Aruwan yace an kakkabe wani sansanin 'yan ta'addan dake Daban Lawal Kwalba a karamar hukumar Igabi bayan sojojin sun ci karfin 'yan bindigan dake gadin wadanda suka yi garkuwa da su.

"Bayan sojojin sun gama da 'yan bindigan sai suka dira maboyarsu tare da ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a daure da kaca. Sojojin sun kwance wadanda aka sacen."

- Aruwan yace.

Kamar yadda Aruwan yace, dakarun sojin sunyi nasarar kwashe wadanda aka sace zuwa asibitin sojoji inda suke karbar taimakon masana kiwon lafiya kafin a sada su da iyalansu.

Yace gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, ya yabawa dakarun sojin kan kokarinsu da kara musu karfin guiwa wurin cigaba da kokarin.

Dakarun Sojin Najeriya Sun Ceto Mutum 6 da Aka Yi Garkuwa dasu a Kaduna

A wani labari na daban, kasa da sa'o'i 48 bayan halaka wadanda suka shirya karantsayen tsaro a Makarantar Horar da Hafsoshin Soji ta Kaduna da satar daliban kwalejin gandun daji, dakarun sojin Najeriya sun ceto wasu mutum shida a yankin Kangon Kadi dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar ranar Litinin, The Nation ta rahoto.

Aruwan yace kamar yadda dakarun suka bayyana karkashin Operation Forest Sanity, sun je aikin kakkabe daji daga Damba zuwa Kangon Kadi kuma tarar da wurin wasu 'yan bindiga a kusa da Kangon Kadi, Labi da kogin Udawa, jaridar Premium Times ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel