Katsina: Yadda Yarinya Mai Shekaru 13 Ta Haddace Qur'ani, Ta Rubuta shi da Hannunta

Katsina: Yadda Yarinya Mai Shekaru 13 Ta Haddace Qur'ani, Ta Rubuta shi da Hannunta

  • Zuwaira Ahmed yarinya ce mai shekaru 13 da ta haddace Qur'ani tare da rubuta shi cikakke fa kanta
  • Ta haddace Qur'anin a cikin shekaru hudu kamar yadda malaminta, Malam Garba Kanya ya bayyana
  • Shugaban karamar hukumar Kafur na jihar Katsina ya bayyana cewa zai tallafawa karatun yarinyar tun daga sakandare hara jami'a

Katsina - Wata yarinya mai shekaru 13 mai suna Zuwaira Ahmed dake kauyen Kagara dake karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina ta haddace tare da rubuta Qur'ani cikakke.

A yayin jawabi a taron da aka shirya domin karrama yarinya a ranar Asabar, Dagacin Mahuta, Bello Abdulkadir, ya bayyana jin dadinsa da farin cikinsa kan wannan cigaban, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Bakatsina
Katsina: Yadda Yarinya Mai Shekaru 13 Ta Haddace Qur'ani, Ta Rubuta shi da Hannunta. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa wannan babban cigaba ne da aka samu a yakin da jihar baki daya balle a fannin ilimin addinin Islama.

Abdulkadir ya kara da yabawa iyaye dake yankin, malamai da shugabannin yankin wurin tarbiyyar yaransu tare da kira garesu da su cigaba da hakan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Danejin Katsinan ya tabbatar da cewa sarakunan gargajiya zasu cigaba da taimakon dukkan abinda ya shafi addini domin cigaba dukkan yankin.

Shugaban karamar hukumar Kafur, Garba Kanya, ya yabawa karatun yarinyar tare da tabbatar da cewa zai tallafawa karatunta tun daga sakandare har jami'a.

Shugaban makarantar Madrasatul Tahfiz, Sheikh Sani Kagara, yace an kafa makarantar ne domin bada ilimin Islama ga yaran yankin.

Kamar yadda ya fadi, yarinyar ta haddace Qur'ani cikin shekaru hudu kuma ya alakanta nasararta da goyon bayan da iyayenta da malamanta suka bata.

A jawabinsa, mahaifin Zuwaira, Ahmed Sani, ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka goyi bayan diyarsa ina yayi kira ga iyaye da su bar yaransu neman ilimin addini da na boko.

Yadda Hannu a Karbar Kudin Fansa har N2b da Alaka da Kungiyar Ta'addanci ta sa aka Kama Mamu

A wani labari na daban, Tukur Mamu, mawallafi kuma mazaunin Kaduna an kama shi a Cairo sakamakon zarginsa da ake da hannu wurin karbar kudin fansa tare da kai wa 'yan ta'adda domin sakin wadanda suka sace, Daily Trust ta tattaro daga majiya mai karfi.

Daily Trust ta rahoto cewa, wasu majiyoyin tsaro sun ce baya ga alaka da 'yan ta'addan Najeriya, Mamu ya shiga hannun hukuma ne saboda alakar da yake da ita mai karfin da wata kungiyar ta'addanci a yankin Sinai dake Misra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel