Yobe: Ɗan Takarar Kujerar Majalisar Tarayya Karkashin PDP a 2023 Ya Rasu

Yobe: Ɗan Takarar Kujerar Majalisar Tarayya Karkashin PDP a 2023 Ya Rasu

  • Wani ɗan takarar majalisar wakilan tarayya a inuwar PDP daga jihar Yobe, Muhammed Bukar, ya rasu ranar Asabar
  • Marigayin ya rasu ne a Asibitin koyarwa na jami'ar jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya bayan fama da rashin lafiya
  • Wata majiya ta bayyana cewa kafin rasuwarsa, Bukar ya jima yana yawo tsakanin ƙasar Indiya da Najeriya domin neman lafiya

Yobe - Ɗan takarar kujerar mamba a majalisar wakilan tarayya karkashin inuwar jam'iyyar Peoples’ Democratic Party (PDP) daga jihar Yobe a zaɓen 2023, Muhammed Bukar, ya riga mu gidan gaskiya.

The Nation ta ruwaito cewa Marigayi Bukar, shi ne ɗan takarar da PDP a tsayar a kujerar ɗan majalisa mai wakiltar Gulani, Gujba da Damaturu dake jihar Yobe, arewa maso gabashin Najeriya.

Dan takarar PDP, Bukar Mohammed.
Yobe: Ɗan Takarar Kujerar Majalisar Tarayya Karkashin PDP a 2023 Ya Rasu Hoto: thenation
Asali: UGC

Bayanai sun yi nuni da cewa labarin rasuwar ɗan siyasan ta fito ne ranar Asabar kuma an ce ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Katsina: Yadda Yarinya Mai Shekaru 13 Ta Haddace Qur'ani, Ta Rubuta shi da Hannunta

Wata majiya daga cikin iyalansa ta bayyana cewa Muhammed Bukar ya rasu ne a Asibitin koyarwa na Jami'ar jihar Yobe, inda ya kwanta jinya na wani ɗan lokaci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka nan wasu bayanai sun ce Marigayin ya rasu ne bayan fama da wata cuta da ta shafi hanta.

Majiya ta tabbatar da cewa Mamacin, wanda tsohon shugaban ƙungiyar kwadugo ne, ya jima yana shige da fice zuwa Asibitin Indiya da Najeriya domin kula da lafiyarsa kafin lokacinsa ya cika.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ya rage watanni ƙasa da shida a fafata babban zaɓen 2023 kuma 'yan kwanaki kaɗan kafin fara kamfe na takarar shugaban ƙasa.

Sarauniyar Ingila ta rasu ranar Alhamis

A wani labarin kuma kun ji cewa Sarauniyar Ingila, Elizabeth II, Ta Rasu Tana da Shekaru 96 a duniya

Kara karanta wannan

2023: Hanya Ɗaya Da Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar Ya Magantu

Rahotanni daga majiyoyi sun shaida cewa, masarautar Ingila ta tashi da bakin labarin jirkicewar lafiyar sarauniya, lamarin da yasa likitoci ke kai komo a kanta.

A wata sanarwar da masarautar ta Ingila ta fitar, an sanar da rasuwar sarauniyar da yammacin Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel