Cikakkun Jerin Sunayen Sabbin Shugabannin Kungiyar Daliban Najeriya Na Kasa

Cikakkun Jerin Sunayen Sabbin Shugabannin Kungiyar Daliban Najeriya Na Kasa

  • Kwamitin shirya babban taron kungiyar dalibai ta kasa ya saki cikakkun sunayen sabbin zababbun shugabannin NANS
  • Kwamitin na NANS ya kuma nemi jami'an tsaro da su kama dukkanin masu yiwa shugabannin kungiyar sojan gona
  • Usman Umar Barambu, dalibin jami’ar tarayya ta Dutse shine sabon shugaban kungiyar NANS

Abuja - Kungiyar daliban Najeriya ta kasa (NAN) ta saki cikakkun sunayen sabbin shugabanninta da aka zaba a babban taronta da ya gudana a karshen makon jiya.

Sai dai kuma, kwamitin NAN ya bukaci jami’an tsaro da su kama sojojin gona da ke daukar kansu a matsayin sabbin shugabannin kungiyar, jaridar PM News ta rahoto.

Shugaban NANS
Cikakkun Jerin Sunayen Sabbin Shugabannin Kungiyar Daliban Najeriya Na Kasa Hoto: @SolaOmoniyi22
Asali: Twitter

Kwamitin shirya babban taron NANS ne ya saki jerin sunayen a daidai lokacin da ake tsaka da rikicin cewa kungiyar daliban ta gudanar da zabe da ya samar da shugabanni biyu.

Sai dai kuma, kwamitin a cikin wata takarda da ta gabatarwa manema labarai a ranar Litinin, ta ce Usman Umar Barambu, dalibin jami’ar tarayya ta Dutse shine sabon shugaban NANS.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya samu kuri’u 292 wajen kayar da Lawal wanda ya samu kuri takwa, Jirin Idris mai kuri’u hudu da Nanven Haruna mai kuri’u biyu.

Kwamitin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugabansa, Bappare Muhammad; sakatare, Pedro Obi; magatakarda, Adeyemi Azeez da kuma shugaban kwamitin tsara sanarwa, Usman Ayuba.

Ga jerin sunayen sabbin shugabannin kungiyar kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto a kasa:

1. Usman Umar Barambu – Zababben shugaba

2. Attah Nnalue Felix – Zababben shugaban majalisar dattawa ta kungiyar

3. Usman Baba Kankia – Zababben babban sakatare

4. Victor W C Ezenagu – Zababben mataimakin shugaba

5. Akinteye Babatunde – Zababben mataimakin shugaba na waje

6. Suleiman Muhammad Sarki – Zababben mataimakin shugaba kan ayyuka na musamman

7. Giwa Yisa Topnotch – Zababben jami’in labarai na kasa

8. Chinyelu Chinelo Okolie – Zababben ma’ajin kungiyar na kasa

9. Vanessa Egbeahie – Mataiumakin shugaba kan harkokin cikin makaranta

10. Mohammed Shehu

11. Ossai Chika – Zababben mataimakin babban sakatare

12. Godwin Asuquo – Zababben sakataren kudi

13. Salawudeen Kamorudeen – Zababben daraktan tafiye-tafiye da canji

14. Umar Afkhawa – Zababben daraktan wasanni

15. Ekundina Segun Elvis – Mataimakin shugaban majalisar dattawan kungiya

16. Olatunji Baki – Zababben magatakarda

Yanzu-Yanzu: Kwamiti Babban Taron NANS Ya Bayyana Sakamakon zaben Shugaba Na Kasa

A baya mun kawo cewa, Kwamitin shirya babban taro na kungiyar daliban Najeriya ya saki jerin sunayen wadanda suka lashe zaben kungiyar daliban na ranar Asabar.

Sakamakon zaben ya haifar da rikici a ranar Asabar bayan an samu shugabannin kungiyar daga tsagi biyu.

A karshe an magance takaddaman yayin da kwamitin ya ayyana Usman Barambu a matsayin zababben shugaban kungiyar, jaridar Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel