Yanzu-Yanzu: Kwamiti Babban Taron NANS Ya Bayyana Sakamakon zaben Shugaba Na Kasa

Yanzu-Yanzu: Kwamiti Babban Taron NANS Ya Bayyana Sakamakon zaben Shugaba Na Kasa

  • Usman Barambu ya lashe zabe, ya zama zababben shugaban kungiyar daliban Najeriya
  • Kwamitin shirya babban taro na kungiyar ne ya ayyana Barambu a matsayin zababben shugaba a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin
  • Ya samu kuri'u 292 wajen kayar da babban abokin hamayyarsa, Faruk Lawal, wanda ya samu kuri’u takwas

Abuja - Kwamitin shirya babban taro na kungiyar daliban Najeriya ya saki jerin sunayen wadanda suka lashe zaben kungiyar daliban na ranar Asabar.

Sakamakon zaben ya haifar da rikici a ranar Asabar bayan an samu shugabannin kungiyar daga tsagi biyu.

Barambu
Yanzu-Yanzu: Kwamiti Babban Taron NANS Ya Bayyana Sakamakon zaben Shugaba Na Kasa
Asali: Twitter

A karshe an magance takaddaman yayin da kwamitin ya ayyana Usman Barambu a matsayin zababben shugaban kungiyar, jaridar Punch ta rahoto.

Barambu ya samu kuri’u 292 wajen kayar da babban abokin hamayyarsa, Faruk Lawal, wanda ya samu kuri’u takwas kacal.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban CAN ya magantu kan abin da ya kamata fastoci su yi a lamarin jam'iyya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran yan takarar shugabancin kungiyar da aka lissafa a cikin sanarwar da kwamitin ya fitar a ranar Litinin sun hada da Jibrin Idris mai kuri’u hudu da Nanven Haruna mai kuri’u biyu.

Sauran ‘yan takarar shugaban kasa da aka lissafa a cikin sanarwar ranar Litinin din da ta gabata na kwamitin, wanda wakilinmu ya samu, sun hada da Jibrin Idris (da kuri’u hudu) da Nanven Haruna ( kuri’u biyu).

Dan Jami'ar Bayero da Dan Jami'ar FUD: Wanne ne sahihin sabon Shugaban Kungiyar Dalibai NANS

A baya mun ji cewa Kwamred Umar Farouq Lawal daga Jami'ar Bayero University BUK dake jihar Kano yana ikirarin cewa shi ya zama sabon shugaban kungiyar daliban Najeriya NANS.

Yayinda dan jami'ar tarayya dake Dutse, Usman Umar Barambu, ke ikirarin cewa shine ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Rikici ya barke tsakanin bangarorin kungiyar kare hakkin daliban biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel