Gwamnatin Buhari Ta Dakatar da Shirin Kara Haraji Ga Kamfanonin Sadarwa a Najeriya

Gwamnatin Buhari Ta Dakatar da Shirin Kara Haraji Ga Kamfanonin Sadarwa a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirinta na kara yawan kuɗin kira, tura sako da sayen Data a Najeriya
  • Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Pantami, wanda ya sanar da haka, yace dama baya goyon bayan shirin ƙara harajin kan harkokin sadarwa
  • A baya dai ministar kasafin kuɗi, Zainab Ahmed, ta jaddada cewa ba gudu ba ja da baya a karin harajin duk da Pantami ya soki shirin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya ta dakatar da shirinta na ƙara yawan Harajin da take karɓa daga kiran waya, Data da sauran ayyukan sadarwa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami, shi ne ya bayyana haka ranar Litinin a wurin taron kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan harajin aiki da ɓangaren tattalin arzikin zamani a Abuja.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Buhari Tace Ta Magance Mafi Munin Matsalar Tsaro a Najeriya

Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Pantami.
Gwamnatin Buhari Ta Dakatar da Shirin Kara Haraji Ga Kamfanonin Sadarwa a Najeriya Hoto: Prof. Isa Pantami/facebook
Asali: Facebook

Sheikh Pantami yace dama tuni aka mamaye ɓangaren sadarwar zamani da yawan haraji kala daban-daban da ya wuce ƙima, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ministan ya ƙara da cewa tun can baya shi a karan kansa baya goyon bayan ƙara yawan harajin, wanda babu kokwanto zai ƙara tsadar kiran wayar salula, Data da sauran harkokin sadarwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda FG ta shirya ƙara Harajin

A kwanakin baya, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda gwamnatin tarayya ta hannun ofishin kasafin kuɗi ta sanar da shirinta na kara harajin.

Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa FG zata aiwatar da shirin karin harajin a shekarar 2023 dake tafe.

A wata sanarwa ta hannun mai taimaka mata kan harkokin watsa labarai, Tanko Abdullahi, ta kafa hujja da dokar kudi 2020 a matsayin abinda ya basu damar ƙara harajin.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Tun a wancan lokaci Pantami ya yi watsi da lamarin kuma duk da haka Ministan tace ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen fara aiwatar da shirin kan kiran murya, tura sako da Data.

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya tace ta magance yawaitar kalubalen tsaro a baki ɗaya sassan Najeriya amma akwai sauran yaƙi

Gwamnatin shugaba Buhari tace Sojoji da sauran hukumomin tsaro na samun nasara a kokarin dawo da zaman lafiya a Najeriya.

Ministan labarai, Lai Muhammed, ya ce duk da akwai sauran yaƙi amma za'a iya cewa an magance mafi munin matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel