Gwamnan Abiya Ya Yi Barazanar Maka Wani Dan Majalisa a Kotu Kan Barazanar Kisa

Gwamnan Abiya Ya Yi Barazanar Maka Wani Dan Majalisa a Kotu Kan Barazanar Kisa

  • Gwamnan jihar Abiya, Dr. Okezie Ikpeazu, yace ba zai tsaya ya zuba ido wasu mutane su jefa rayuwarsa da ta iyalansa a haɗari ba
  • Bayanai sun nuna ana zargin Hon. Ginger Onwusibe, ɗan majalisar jiha da yi wa gwamnan barazana da rayuwa a wani taro bayan ya fice PDP
  • Sai dai ɗan majasar ta bakin kakakin kamfensa, ya musanta zargin, yace hukumar yan sanda ta gayyaci mai gidansa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abia - Gwamna jihar Abia, Dr. Okezie Ikpeazu, ya sha alwashin maka ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Isiala Ngwa ta arewa a majalisar dokokin jiha, Hon. Ginger Onwusibe, kan zargin barazana ga rayuwarsa.

Onwusibe, wanda ya fice daga PDP zuwa Labour Party domin neman takarar kujerar majalisar wakilan tarayya a 2023, ana zarginsa da yi wa gwamna barazanar rayuwa a wani taro da ya gudana a yankin Obingwa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023

Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya.
Gwamnan Abiya Ya Yi Barazanar Maka Wani Dan Majalisa a Kotu Kan Barazanar Kisa Hoto: Vanguardngr.com
Asali: UGC

Sai dai a rahoton jaridar Vanguard, ɗan majalisar ya musanta zargin inda ya jaddada cewa ko da wasa bai taɓa yi wa gwamna Ikpeazu barazana da rayuwa ba.

A makon da ya gabata hukumar yan sanda ta gayyaci Hon. Onwusibe kan batun. Kakakin Kamfen ɗin ɗan majalisan yace da isar mai gidansa Hedkwatar 'yan sanda aka gaya masa lauya a madadin gwamna ne ya shigar da ƙorafinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki gwamna ya yi shirin ɗauka?

A wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na ofishin gwamna, Sir Onyebuchi Ememanka, ya fitar, Ikpeazu, ya bayyana cewa zai ɗauki matakin shari'a kan Onwusibe, don karkare batun a Kotu.

Gwamnan ya sha alwashin cewa ba zai bar lamari irin wannan a iska ba domin ba wani cikakken ɗan kasa da zai zuba ido ana yi wa dakarun tsaronsa barazana ba tare da ya yi komai ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Fallasa Wanda Wike da Wasu Gwamnoni Suka Amince Ya Gaji Buhari a 2023

Sanarwan tace:

"An jawo hankalin gwamnan Abiya, Dr. Okezie Ikpeazu, kan barazanar kai farmaki ga mutanensa, iyalai har da Ofishinsa na gwamna wanda wasu mutane suka yi."
"Kowa ya sani an yi wannan cin kashin a baya daga yanzu gwamna zai bi duk hanyoyin da doka ta tanaza domin kare mutanensa, iyalai da Ofishinsa daga duk wasu ayyuka da zasu jefa ryuwarsa da ta iyalansa a haɗari."
"Saboda haka, gwamna Ikpeazu zai ɗauki matakin shari'a kan Hon. Ginger Onwusibe, domin kawo karshen lamarin a gaban Kotun doka."

A wani labarin kuma Kotu Ta Soke Zaɓen Kananan Hukumomin Jihar Ebonyi Wanda APC Ta Lashe

Babbar Kotun tarayya da ke zama a Abakaliki ta soke zaɓen kananan hukumomin jihar Ebonyi wanda aka gudanar ranar 30 ga watan Yuli.

Alkalin Kotun, Mai shari'a Rilman Fatun, ya ce zaben ya saba wa tanadin sabon kundin zaɓen 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel