Gwamnonin Kudu Har da Wike Sun Yi Imani Mulki Ya Koma Yankin a 2023, Umahi

Gwamnonin Kudu Har da Wike Sun Yi Imani Mulki Ya Koma Yankin a 2023, Umahi

  • Gwamnan Ebonyi yace baki ɗaya takwarorinsa na yankin kudancin Najeriya bakinsu ɗaya kan wanda zai gaji Buhari a 2023
  • Gwamnan ya bayyana cewa Wike da sauransu sun zauna tun a baya sun cimma matsaya kan tsarin karɓa-karba
  • Umahi na ɗaya daga cikin waɗan da ake zargin sun gana da Wike a Landan, amma ya musanta rahoton

Abuja - Gwamnan jihar Ebonyi, Injiniya Dave Umahi, ya kalubalanci gwamnonin kudu da su fito su gaskata cewa baki ɗayansu suna bayan shugaban ƙasa na gaba ya fito daga kudu kamar yadda gwamna Wike ke fafutuka yanzu.

A wata hira da kafar Talabijin ta Aris tv, Umahi ya bayyana cewa tun farko gwamnonin Kudu sun cimma matsayar cewa ya kamata a rika karɓa-karɓa da kujerar shugaban ƙasa.

Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi.
Gwamnonin Kudu Har da Wike Sun Yi Imani Mulki Ya Koma Yankin a 2023, Umahi Hoto: Dave Umahi
Asali: Facebook

Haka nan kuma gwamna Umahi, mamba a jam'iyyar APC, ya musanta rahoton dake yawo cewa ya gana da gwamna Wika Landan, inda ya kara da cewa yana nan matsayinsa na aboki.

Jaridar Vanguard ta rahoto Umahi na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ban jima da dawowa daga tafiyar kwana Takwas ba daga Dubai kuma na karanta da kafafen watsa labarai cewa gwamna Nyesom Wike da wasu sun gana a Landan. Ban je Landan ba, hukumar shige da fice ta sani."
"Wike ɗan uwana ne kuma aboki, mun ɗan samu saɓani kuma idan irin haka ta faru da yuwuwar a fusata amma ba ta har abada ba. A baya mu manyan abokan juna ne har zuwa lokacin da na bar PDP."
"Kun san cewa idan babban abokinka ya guje ka dole gaji ba daɗi, amma mun sasanta da jimawa mun cigaba da abotarmu."

Wane ɗan takara Wike da gwamnonin kudu ke goyon baya?

Gwamna Umahi ya kara da cewa baki ɗaya gwamnonin kudancin Najeriya bakin su ɗaya, suna son a tabbatar da mulkin karɓa-karɓa ne a zaɓe mai zuwa.

"Bari na faɗa muku, gwamna Wike da sauran gwamnonin kudu sun amince mulki ya koma hannun ɗan kudu kuma wannan ne ya hana PDP zama sakat duk da bana son magana kan wasu jam'iyyu."
"Kafatanin gwamnonin kudu (Idan baku manta ba) sun zauna suka cimma matsayar a riƙa karba-karban kujerar shugaban kasa tsakanin kudu da arewa kuma ina ganin kowanensu yana girmama matakin."
"Wike mutumin kirki ne, yana da zuciya mai kyau, mutum ne na gari, duk waɗan nan abubuwa ba daga karkashin zuciya suke fito wa ba, daga harshe ne yayin da ake cikin fushi."

A wani labarin kuma Wani Babban Jigon APC da Dubbannin Magoya Baya Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Na hannun daman tsohon gwamnan Ogun kuma jigo a APC ya tattara masoyansa sun koma jam'iyyar PDP.

Babatunde Onakoya, yace bisa tilas aka masa kora da hali saboda yawan rikici da yaƙi karewa a jam'iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel