INEC Ta Sanar Da Ranar Wallafa Ta Karshe Na Sunayen Dukkan Yan Takara A Zaben 2023

INEC Ta Sanar Da Ranar Wallafa Ta Karshe Na Sunayen Dukkan Yan Takara A Zaben 2023

  • Hukumar shirya zabe ta INEC za ta fitar da sunayen wadanda za'a gani ranar zabe a 2023
  • Hukumar INEC za ta gudanar zaben shugaban kasa ranar 28 ga watan Febrairu 2023 sannan na gwamna bayan makonni 2
  • Shugaba Buhari ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa ba zai yi katsalandan a zaben 2023 ba

Abuja - Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, za ta saki sunayen dukkan yan takaran da zasu yi musharaka a zaben kasa na shekarar 2023.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja inda ya halarci taron kungiyar Centre for Democracy and Development (CDD).

A cewarsa, hukumar zata saki sunayen yan takaran shugaban kasa, Sanatoci da yan majalisar wakilai ranar 20 ga Satumba, 2022, rahoton Channels.

Kara karanta wannan

Nan Da Watanni 6 Yan Najeriya Zasu Yabawa Gwamnatina, Buhari

Yayinda za'a saki na gwamnoni da majalisar jiha ranar 4 ga Oktoba.

Mahmoud
INEC Ta Sanar Da Ranar Wallafa Ta Karshe Na Sunayen Dukkan Yan Takara A Zaben 2023 Hoto: INEC
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika ya bayyana ranar da za'a fara kamfe da kuma halin rashin tsaron da ake ciki a wasu sassan Najeriya, riwayar TheNation.

A cewarsa:

"Harkokin zaben 2023 zasu yi zafi a watan nan. Nan da ranar 19 ga Satumba 2022, hukumar zata wallafa sunayen karshe na yan takaran shugaban kasa, Sanatoci da Majalisar wakilai, kamar yadda sashe 32(1) na dokar zabe ya tanada."
"Bayan haka ranar 4 ga Oktoba za'a saki sunayen yan takaran kujerar gwamna da yan majalisar jiha."
"Za'a fara kamfe ranar 28 ga Satumba, 2022. Idan aka fara, muna kira ga jam'iyyun siyasa da yan takara su mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci."

Nan Da Watanni 6 Yan Najeriya Zasu Yabawa Gwamnatina, Buhari

A wani labarin kuwa, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa cikin watanni shida masu zuwa, yan Najeriya zasu yabawa gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) saboda yancin da za'a basu wajen zaben wanda suke so.

Kara karanta wannan

An Dage Zaman Yan Takaran Shugaban kasan APC Da Tinubu, Sun Ki Zuwa

Buhari ya bayyana hakan ne ranar Talata yayinda ya karbi bakuncin kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC karkashin jagorancin gwamnan Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

Shugaban kasan yace gwamnatinsa ba za ta bari a ci mutuncin yan Najeriya a zaben 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel