Nan Da Watanni 6 Yan Najeriya Zasu Yabawa Gwamnatina, Buhari

Nan Da Watanni 6 Yan Najeriya Zasu Yabawa Gwamnatina, Buhari

  • Shugaba Buhari ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa ba zai yi katsalandan a zaben 2023 ba
  • Buhari ya tabbatarwa yan Najeriya nan da watanni shida masu zuwa, yan Najeriya zasu yabawa gwamnatinsa
  • Hukumar INEC ta shirya zaben shugaban kasa ranar 28 ga watan Febrairu 2023

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa cikin watanni shida masu zuwa, yan Najeriya zasu yabawa gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) saboda yancin da za'a basu wajen zaben wanda suke so.

Buhari ya bayyana hakan ne ranar Talata yayinda ya karbi bakuncin kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC karkashin jagorancin gwamnan Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, rahoton Vanguard.

Shugaban kasan yace gwamnatinsa ba za ta bari a ci mutuncin yan Najeriya a zaben 2023 ba.

A cewarsa:

"Ba zamu bari kowani mutum yayi amfani da dukiyarsa wajen cin mutuncin yan Najeriya ba. Ba zamu yarda a yiwa mutane barazana da kudi ba."

Kara karanta wannan

An Dage Zaman Yan Takaran Shugaban kasan APC Da Tinubu, Sun Ki Zuwa

"Cikin watanni shida, yan Najeriya zasu yabawa gwamnatin APC saboda zasu gane mu masu gaskiya ne kuma muna ganin mutuncinsu."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

BUhari
Nan Da Watanni 6 Yan Najeriya Zasu Yabawa Gwamnatina, Buhari Hoto: Buhari
Asali: Facebook

Sunayen ‘Yan Siyasa da Bara-Gurbi da Buhari Ya Nemi Ya Cusa a INEC Sun Fito Fili

A makon da ya gabata Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar dattawan Najeriya sunayen wadanda za a ba mukaman REC a INEC.

Legit.ng ta fahimci wannan takarda tana kunshe da sunayen mutane 19 da shugaban kasa ya zaba.

A cikin wadanda aka zakulo, mutum biyar za su koma kan kujerunsu ne idan an amince da nadinsu, yayin da ragowar za su dare kujerar a karon farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida