An Dage Zaman Yan Takaran Shugaban kasan APC Da Tinubu, Sun Ki Zuwa
- An shirya tara dukkan yan takara a zaben fidda gwani don hada kai wajen ganin Tinubu ya ci zabe
- Babu wanda ya halarci zaman cikin dukkan yan takaran kuma hakan ya tilasta dage zaman
- Tinubu ya lallasa wadannan yan takara a zaben fidda gwanin APC yayinda ya samu kuri'u 1,271
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Zaman da aka shirya yau Laraba na mutum 21 da suka yi takara a zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasa karkashin APC a Abuja ya fuskanci matsala.
An shirya zaman ne misalin karfe biyu na rana a Transcorp Hilton don tattauna yadda zasu hada kai don nasarar Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023 amma an dage.
Har yanzu ba'a bayyana ainihin dalilin da yasa aka dage zaman ba, amma an tattaro cewa yawancin yan takaran basu halarci zaman ba.
Wanda ya shirya zaman, Fasto Nicolas Felix, ya bayyana cewa an dage zaman zuwa wani lokaci.
A wasikar da ya aikewa Vanguard:
"Barka dai ranka shi dade. Ana sanar da kai cewa zaman tsaffin yan takaran shugaban kasa karkashin All Progressives Congress (APC), da aka shirya ranar Laraba, 31 ga Agusta, an dage."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Za'a sanar da sabuwar ranar ganawan nan ba da dadewa."
Yan takara sun yi watsi da zaman
An tattaro cewa wasu yan takaran ko amsa gayyatar basu yi ba.
Wata majiya tace:
"Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbaji ya yi tafiya. Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ko amsa gayyatar bai yi ba, hakazalika Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi,”
Kashim Shettima Ya Nuna Yadda Za a Raba Ayyuka Muddin Tinubu Ya Hau Mulki
A wani labarin kuwa, Kashim Shettima wanda shi ne ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa a APC, yace zai maida hankali ga tsaro idan suka kafa gwamnati.
Premium Times tace Sanata Kashim Shettima ya sha alwashin idan suka yi nasara a zaben 2023, zai kula da sha’anin tsaro domin kawo zaman lafiya.
Tsohon gwamnan na Borno ya bayyana wannan a wajen babban taron NBA na kasa da aka yi a Legas, inda ya gabatar da jawabi a gaban Lauyoyi.
Shettima ya fadawa mahalarta zaman da aka yi a farkon makon nan cewa jagoranci jami’an tsaro wajen ganin an samu zaman lafiya a Najeriya
Asali: Legit.ng