Yadda Na Kusa Rasa Muryata Bayan Na Yi Magana Da Wani Dan Damfara Da Ya Aike Mun Katin Waya

Yadda Na Kusa Rasa Muryata Bayan Na Yi Magana Da Wani Dan Damfara Da Ya Aike Mun Katin Waya

  • Wata budurwa ta ja hankalin mutane a kan wata sabuwar hanya da miyagu ke bi don cutar da bayin Allah da basu ji ba basu gani ba
  • Matashiyar ta bayyana cewa saura kiris ta rasa muryarta don har ta zama bebiya na wucin gadi bayan ta yi magana da wani da ya aika mata katin waya bisa kuskure
  • Mutumin ya kira da nufin yi mata godiya bayan ta mayar masa da katinsa sai kuma ya ba mahaifinsa ya gode mata bayan ta katse kiran, sai ta nemi muryarta ta rasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Wata matashiya yar Najeriya ta bayyana yadda ta kusa zama bebiya bayan ta yi magana da wani dan damfara.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, matar ta ce ta amsa kiran waya daga wani da ya yi ikirarin aika kati zuwa layinta.

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Zama Mai Goge-goge Bayan Kammala Digiri Na Biyu, Allah Ya Sauya Rayuwarta A Karshe

Mai kiran wayan ya yi ikirarin cewa zai aikawa wani kati ne amma sai ya yi kuskuren lamba ya aika zuwa nata layin.

Budurwa
Yadda Na Kusa Rasa Muryata Bayan Na Yi Magana Da Wani Dan Damfara Da Ya Aike Mun Katin Waya Hoto: lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

Sai budurwar tayi masa alkawari cewa ba za ta yi amfani da katin ba idan ya shigo wayarta. Kwatsam sai ga katin ya shigo layinta kuma sai kuma sai mutumin ya sake kira, kuma kamar yadda tayi alkawari bata yi amfani da shi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan nan sai mutumin ya sake kira don yi mata godiya sannan ya bayyana cewa mahaifinsa na son magana da ita.

Ta ce da fari ta ki amincewa amma daga baya sai ta yarda sannan suka yi magana da mahaifin nasa wanda ya yi mata godiya sannan ya koma yi mata wasu tambayoyi game da kanta.

Budurwar ta kuma bayyana cewa hakan ya fara bata tsoro sannan ta yi kokarin katse hirar amma mutumin ya ci gaba da tafiya.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Yi Bidiyon Surar Jikina Ya Fita Har Aka Koreni A Harkar Fim - Safara’u Kwana Casa'in

Ta ce:

“Ya ce ‘yata ban san har yanzu akwai irinki a duniya ba. Allah Ya Yi maki albarka. Nace Amin. Ya ce ‘Daga Talauci zuwa Talauci’. Ban ma ji abun da ya fadi ba. Kanwata wacce ta ji shi ce tace ‘Allah ya kiyaye’.
"Ya ci gaba sannan ya tambayeni sunana. Nace masa bai da amfani. Ya tambayeni a ina nake zama. Nayi masa karya cewa a Lagas nake zama. Sai yace toh me nake yi? Nace hakan na da amfani? Ka yi mun godiya.. Ina katse kiran a nan take na rasa gane kaina. Kamar ina so na amayo wani abu. Daga nan na rasa muryata.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

brightshine9311 ta ce:

"Ba karya take yi ba! Dan Allah mu dunga taka-tsan-tsan. Abubuwa na faruwa faa."

faith.ubi ta ce:

"Irin abun da aka yiwa makwabciyata a gabana."

amalianhair16 ta yi martani:

"Allah ya taimakemu ."

Kara karanta wannan

Dan Shekaru 71 Ya Koma Makarantar Firamare, Bidiyo Ya Nuno Sa A Aji Tare Da Jikokinsa

Yadda Yan Mata Suka Warware Surkullen Da Kawarsu Ta Yiwa Saurayinta, Ta Daure Shi A Kwalba

A wani labarin, wata budurwa da ba a gane ko wacece ba ta sha caccaka a wajen kawayenta a soshiyal midiya kan saka sunan saurayinta a da tayi a cikin kwalba.

A cewar yan matan a wani bidiyo da ya yadu, sun yi ikirarin cewa budurwar wacce ta kasance kawarsu ta daddaure kwalban kafin ta jefa shi a cikin rafi.

Yayin da suke kwancewa kawar tasu zani a kasuwa kan abun da ta aikata, sun koka cewa rayuwarsu suma tana cikin hatsari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel