Yadda Yan Mata Suka Warware Surkullen Da Kawarsu Ta Yiwa Saurayinta, Ta Daure Shi A Kwalba

Yadda Yan Mata Suka Warware Surkullen Da Kawarsu Ta Yiwa Saurayinta, Ta Daure Shi A Kwalba

  • Wasu yan mata sun kwancewa muguwar kawarsu zani a kasuwa kan sanya sunan wani saurayi da tayi a cikin kwalba sannan ta jefa a ruwa
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu, yan matan sun ciro kwalban sannan suka warware zaren da budurwar ta daddaure kwalban da shi
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani a kan bidiyon inda da dama suka nuna rashin jin dadinsu kan abun da budurwar tayi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata budurwa da ba a gane ko wacece ba ta sha caccaka a wajen kawayenta a soshiyal midiya kan saka sunan saurayinta a da tayi a cikin kwalba.

A cewar yan matan a wani bidiyo da ya yadu, sun yi ikirarin cewa budurwar wacce ta kasance kawarsu ta daddaure kwalban kafin ta jefa shi a cikin rafi.

Kara karanta wannan

Bayan Shafe Shekaru 3 Tana Aiki A Kasar Waje, Budurwa Ta Dawo Gida Najeriya, Ta Zama Mai Jiran Shago

Surkulle
Idanun Wani Ya Bude: Yadda Yan Mata Suka Warware Surkulen Da Kawarsu Ta Yiwa Saurayinta, Ta Daure Shi A Kwalba Hoto: @bcrworldwide / Anna Frank
Asali: Instagram

Yayin da suke kwancewa kawar tasu zani a kasuwa kan abun da ta aikata, sun koka cewa rayuwarsu suma tana cikin hatsari.

“Wannan yarinyar na da karfin hali. Ya kamata mu boye kayanmu saboda wannan yarinyar na iya amfani da shi wajen yin asiri,” cewar daya daga cikin yan matan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan sun warware kwalban tare da bude shi, sai suka bayyana sunan saurayin a matsayin Favour.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Heartwinners_autos ta rubuta:

“Idanun wani sun bude.”

Hurleyexchangee ya yi martani:

“Me yasa kuke bata asirin kawarku. Dukkanku ne kuke yin asiri.”

Greg_himself ya yi martani:

“Yan Najeriya za su kasheni wata rana da duk wadannan canfe-canfen.”

Jenny_heebert16 ta yi martani:

"Ahh sunan yayana kenan faaa.”

Tsoffin Maza Sun Fi Iya Soyayya: Matashiya Yar Shekaru 30 Da Ta Auri Dan Shekaru 80

Kara karanta wannan

Daga Daki Daya Zuwa Gida Mai Kyau: Ma’auratan Da Ke Tare Tun Suna Talakawa Sun Kudance, Bidiyonsu Ya Yadu

A wani labarin, wata mata da ta dulmiya a cikin soyayya ta baiwa mutane da dama mamaki bayan ta bayyana irin soyayyar da suke sha da sahibinta, wanda zai iya yin kaka da ita.

Matashiyar wacce ta fito da Mudaka, yankin Kudancin Kivu a damokradiyyar Kongo, ta ce soyayya babu ruwansa da banbancin shekaru kuma bai da iyaka.

Tsawon shekaru biyu kenan da Mwamini ta auri burin ranta Katembela Etienne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel