Allah Ka Rabumu Da Mugun Miji: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Addu’a Ya Ja Hankali

Allah Ka Rabumu Da Mugun Miji: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Addu’a Ya Ja Hankali

  • Wani bidiyon karamar yarinya tana addu’an samun miji nagari da kasuwanci mai albarka ya yadu
  • A yayin addu’an, an jiyo muryar wata babba tana ihun “Amin” yayin da yarinyar ke zagaye wani shago
  • Yan Najeriya da dama da suka yi martani ga bidiyon sun ce lallai yarinyar na kwaikwayon yadda mahaifiyar ke addu’a ne a koda yaushe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Wata karamar yarinya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce da yanayin addu’anta a shafukan soshiyal midiya. Bidiyon wanda @instablog9ja ya wallafa, an gano yarinyar tana addu’a a gaban wasu manya.

A cikin bidiyon, ta rike wani dan karamin kwalba a wanda shine a matsayin lasifika yayin da take yiwa wadanda ke wajen addu’an samun miji nagari.

Karamar yarinya
Allah Ka Rabumu Da Mugun Miji: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Addu’a Ya Ja Hankali Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Nasara a kasuwanci, miji da ‘ya’ya

Ta kara da cewa kasuwancin iyalinta zai bunkasa sannan ya habbaka sosai. Yarinyar ta bayyana cewa duk wanda ke nufinsu da sharri a kasuwancin zai koma kansa.

Kara karanta wannan

Abincinki Ko Dadi Babu: Karamar Yarinya Ta Yiwa Mahaifiyarta Ba’a A Bidiyo Mai Ban Dariya, Uwar Ta Yi Martani

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan ta yi addu’a kan kasuwancinsu, sai ta bayyana cewa gidansu zai cika da arzikin ‘ya’ya da albarka.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

official_richimayo ya ce:

“karamar yarinya na addu’an samun miji, amino o.”

oliviaglloww ta ce:

“Wannan addu’an ya fi karfin shekarunta faaa, me kunnuwana suka jiye mun.”

alberts_grill ta ce:

“Tana kwaikwayon addu’o’in mahaifiyarta…Ina zaton babu mahaifi a rayuwarta.”

Abincinki Ko Dadi Babu: Karamar Yarinya Ta Yiwa Mahaifiyarta Ba’a A Bidiyo Mai Ban Dariya, Uwar Ta Yi Martani

A wani labarin, wani bidiyo mai ban dariya wanda ya yadu a soshiyal midiya ya nuno yadda wata uwa da diyarta suke yiwa junansu ba’a.

Sun shiga wani gasa yar yayi da ke yawo TikTok wanda ya bukaci mutane biyu ko fiye da haka su yi magana a kan junansu.

Kara karanta wannan

Ya Guje Mu Saboda Baya Son Tagwaye: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Da Yan Biyunta Ya Ba Da Mamaki

Da take martani game da diyar tata, sai uwar ta bayyana cewa yarinyar na da surutu kuma tana fitsarin kwance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel