An Damke Mata Uku Da Suka Sayar Da Yan Biyun MaiJego Sannan Suka Kasheta

An Damke Mata Uku Da Suka Sayar Da Yan Biyun MaiJego Sannan Suka Kasheta

  • Wasu mata a jihar Enugu sun hada baki da maijego wajen sayar da jariranta kuma suka kasheta bayan amsan kudi
  • Hukumar yan sanda tace an gurfanar da wadannan mata uku gaban kuliya kuma za'a hukuntasu
  • Harkan sayar da jarirai ya zama ruwan dare a Najeriya musamman kudancin kasar

Enugu - Hukumar yan sanda a jihar Enugu ta gurfanar da wasu mata uku kan zargin laifin sayar da jarirai yan biyun da wata maijego ta haifa sannan suka kasheta.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, a jawabin da ya fitar ranar Juma'a ya bayyana cewa an gurfanar da wadannan mata ne bayan kammala bincike.

A cewarsa, an damke wadannan Matan ne ranar 26 a Yuli bayan rahoton da hukumar ta samu na cewa ana zargin sun sayar da jariran wata mata mai suna, Chinenye Odoh, wacce suka kashe daga baya.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Matar Aure Da Kashe Mijinta A Jihar Kebbi, Yan Sanda Sun Damketa

Matan sune Cynthia Ukorie, 25; Pauline Onyia, 56; da Ijeoma Aroh, 39.

A cewar rahoton TheCable, sun hada baki da maijegon wajen sayar da jariran bayan haifensu.

Duk da cewa Ijeoma Aroh wacce ta kawo masu sayan jariran ta sayar dasu N3m, ta fadawa maijegon cewa N2,350,000 ta sayar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Enugu
An Damke Mata Uku Da Suka Sayar Da Yan Biyun MaiJego Sannan Suka Kasheta
Asali: UGC

Hukumar yan sanda tace bayan gudanar da bincike, ta gano an baiwa maijegon N1.8m cikin kudin, sannan sauran matan biyu Ukorie da Onyia suka kowanne ya samu N50,000.

Daga baya da maijegon ta samu labarin ainihin kudin da aka sayar da jariran sai ta fusata kuma ta bukaci a kara mata kan N1.8m da aka bata.

Sai Ukorie ta baiwa maijegon Masarar mai guba, taci kuma ta mutu.

Alkalin kotu ya dage zaman zuwa ranar 5 ga Oktoba, 2022.

An Kama Wata Mata Ta Sace Yara 3 a Borno Zata Tafi Da Su Legas

Kara karanta wannan

An Cika hannu D Wata Mata Ta Sace Yara 3 a Jihar Borno Zata Tafi Da Su Legas

A wani labarin kuwa, hukumar yan sanda a jihar Borno ta bayyana wata mata mai shekara 46, Insa Henshaw, ranar Alhamis, 25 ga Agusta kan laifin satar yara uku zata gudu da su jihar Legas.

An damke matar ne a tashar mota, rahoton HumAngle.

A cewar yan sanda, an damketa ne makonni uku da suka gabata lokacin da aka ganta tana kokarin hawa motar da yaran.

Hukumar tace mutane a tashan ne suka lura ba tada natsuwa sai suka kira yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel