Har Abada Zan Kaunace Ki: Mawaki Eedris Abdulkareem ga Matarsa da ta Bashi Kyautar Koda

Har Abada Zan Kaunace Ki: Mawaki Eedris Abdulkareem ga Matarsa da ta Bashi Kyautar Koda

  • Sanannen mawakin gambara, Eedris Abdulkarim, ya mika godiyarsa ga Ubangiji kan nasarar da aka samu wurin aikin dashen kodar da aka yi masa
  • Bai tsaya a nan ba, ya kwararo kalaman soyayya da bayyana tsabar kaunar da yake wa matarsa kan sadaukarwar da tayi masa ta hanyar bashi kodarta
  • Ya mika godiya ga 'yan uwa, abokai, masoya da duk masu masa fatan alheri inda yace nan babu jimawa zasu dawo gida garas

Fitaccen mawakin gambara, Eedriss Abdulkareem, ya mika godiyarsa ga matarsa Yetunde kan bashi kyautar kodarta da tayi kuma aka samu nasarar yi masa dashe.

Mawakin ya bayyana godiyarsa ne a wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram a ranar Laraba inda ya kara da cewa zai kaunaceta tare da sonta a koda yaushe.

Eedris Abdulkareem
Har Abada Zan Kaunace Ki: Mawaki Eedris Abdulkareem ga Matarsa da ta Bashi Kyautar Koda. Hoto daga MoMedia
Asali: UGC

Idan za tuna, kamfaninsa na nishadantarwa ya bada bayani kan lafiyar mawakin a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kwamitin Gudanarwar Uwar Jam'iyyar PDP Ta Shiga Ganawar Sirri da Yan Takara

A wata takarda da Honarabul Myke Pam ya fitar, yace an samu nasarar yi wa mawakin dashen kodar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yayin jawabi da kansa, Abdulkareem ya mika godiyarsa ga Ubangiji da kuma dukkan mutanen da suka taimaka aka samu nasarar aikin.

Mawakin gambaran ya rubuta:

"Nagode Ubangiji. Ina mika godiya ga Ubangiji madaukaki da aka samu nasarar aikin dashen kodata a cikin ranakun karshen mako. Sunanshi zai cigaba da daukaka har abada.

"Kalamai ba zasu iya bayyana irin kaunata da sadaukarwata ga matata Yetunde, wacce Ubangiji ya cikasa rayuwata da ita, nake mata ba. Masoyiya, zan cigaba da kaunar ki har abada.
“'Ya'yana, Ubangiji ya karba addu'o'inku. Mama da Baba zasu dawo gida cikin koshin lafiya nan babu dadewa.
"Ga 'yan uwana, kamfanin nishadantarwa Lakreem, abokai, masoya da masu min fatan alheri, ina cewa Allah ya duba mana, zan kuma sake ganinku nan babu dadewa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Hazikin Dan Najeriya Yana Tallan Doya A Landan, Ya Ce Ya Tara N116k Cikin Awanni 4

“Na mika wannan sakon godiyan nen na farko domin godewa Ubangiji kan ni'imar da yayi mana."

Matan tsohon fitaccen mawaki Eedris Abdulkareem zata bashi kodanta

A wani labari na daban, wani na kusa da iyalan mawaki Eedris Abdulkareem ya shaida wa jaridar TheCable Lifestyle cewa matar mawakin ta dauki nauyin ba wa mijinta kodarta bayan an kammala yi masa dukkan nau'ikan gwaje-gwaje.

Abdulkareem, tsohon shahararren mawakin Najeriya, yana fama da ciwon koda.

Ana dai yi wa mawakin wankin koda a wani asibiti da ke Jihar Legas kuma ana sa ran za a yi masa dashen koda ne a karshen watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel