Bidiyon Hazikin Dan Najeriya Yana Tallan Doya A Landan, Ya Ce Ya Tara N116k Cikin Awanni 4

Bidiyon Hazikin Dan Najeriya Yana Tallan Doya A Landan, Ya Ce Ya Tara N116k Cikin Awanni 4

  • Wani dan gajeren bidiyo a TikTok ya nuno wani matashin dan Najeriya yana tallan doya a birnin Landan
  • A cewar mutumin, yana kokarin samun karin kudaden shiga ne don biyan haraji wanda wannan ne dalilinsa na shiga unguwa-unguwa tallan doya
  • Ya ce ya yi nasarar tara N116k na tsawon awanni hudu da ya yi yana tallan doya a cikin wani kwali

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ingila - Duk a kokarin samun karin kudaden shigarsa, wani hazikin dan Najeriya ya fara tallan doya a unguwannin Landan.

A cikin wani bidiyo mai ban sha’awa, an gano mutumin tsaye a kan titi yana siyar da doyansa cike da alfahari da sana’arsa.

Dan Najeriya
Bidiyon Hazikin Dan Najeriya Yana Tallan Doya A Landan, Ya Ce Ya Tara N116k Cikin Awanni 4 Hoto: TikTok/@musty706.
Asali: UGC

Ya tara makudan kudade cikin awanni 4 kacal

A cewar bidiyon, karin kudaden shigan zai taimaka masa wajen biyun haraji a Ingila inda yake da zama.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yan Najeriya Sun Hadawa Matashin Da Ya Yi Shekaru 12 A Kurkuku Kudi Don Ya Fara Sana’ar Wanki Da Guga

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce bayan shafe tsawon awanni 4 a kan hanyar, ya yi nasarar samun N116k na cinikin da ya yi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@Adeola Prosper aka masere ta ce:

“Dan Allah fada mun wurin nima na kawo gala mu yi gwagwarmayar tare.”

@Rita4delta ta ce:

“Idan hukuma ta kama ka koo…Ina baka tabbacin cewa za ka biya kwatankwacin harajin. Ka dauki wannan shawarar daga ma’aikaciyar doka. Ina fatan wannan neman suna ne.”

@Marcus Oshiobughie O ya yi martani:

“Ba a yarda da wannan a unguwannin Ingila.”

@Glory Jimmy ta ce:

“Gaskiya ina bukatar faraway kamar haka faaa saboda kasar nan na so ta kashe mu da haraji.”

“Zan Iya Hada miliyan N10 Duk Wata”: Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ke Mayar Da Sharar Robobi Su Zama Bulo

Kara karanta wannan

Iyayen zaman: Uba ya rufe shagon 'yarsa saboda ta ki amince a tafi da ira Italiya yawon karuwanci

A wani labarin, wani hazikin dan Najeriya ya ce idan har ya samu tallafi yadda ya kamata, zai dunga samun makudan kudade daga aikinsa na yin bulo.

Matashin mai kwazo wanda ake kira da suna Promise yana yin bulo masu kwari wanda ake amfani da su wajen gini da sharar robobi da aka zubar.

Sai dai a cikin wani bidiyo da ya yi, Promise ya ce a yanzu haka bashi da kudaden da zai inganta sana’arsa zuwa matakin samun riba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng