Kudin Haya 2.7m duk shekara, Kudin Diesel N80k: Bidiyon Gidan Mai Dakuna 3 Da Budurwa Ta Gani A Lagas

Kudin Haya 2.7m duk shekara, Kudin Diesel N80k: Bidiyon Gidan Mai Dakuna 3 Da Budurwa Ta Gani A Lagas

  • Wata matashiya, Anagu Nkemjika, ta nunawa jama’a gidan haya mai dakuna uku a jihar Lagas da tsayayyen wutar lantarki da ake biyan naira miliyan 2.7
  • Matashiyar budurwar tace duk da cewar tana son karbar gidan, dillalin yace masu daukan albashi kawai za su ba haya
  • Baya ga kudin hayar, mutum zai dunga biyan N80,000 na man diesel duk wata da karin N600,000 na hidindimu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagas - Wata matashiya yar Najeriya, Anagu Nkemjika, wacce ke neman gidan haya a jihar Lagas ta wallafa bidiyon yawon da ta sha wajen neman gida.

Nkemjika ta bayyana cewa a karshe ta ga irin gidan da take nema kuma kudin hayar gidan duk shekara naira miliyan 2.7 ne kuma yana dauke da dakuna uku.

Budurwa da gida
Kudin Haya 2.7m duk shekara, Kudin Diesel N80k: Budurwa Ta Ga Gidan Haya Mai Dakuna 3 A Lagas Hoto: TikTok/@kem_ji
Asali: UGC

Yan albashi kawai muke so

Ba iya nan abun ya tsaya ba, kudin hayar baya kunshe da kudaden hidindimu N600,000 da kudin man diesel N80,000 duk wata.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Damar Saduwa da Ni, Matar Aure Ta Faɗa Wa Kotu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matashiyar ta cika da farin ciki a lokacin da aka bata fom don ta cike a matsayin mai karbar haya sai dai kuma murna ta koma ciki lokacin da suka yi watsi da bukatarta na karbar gidan saboda ita yar kasuwa ce. A cewarta, yan albashi kawai suke so.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

Anwan Abasiubong ya ce:

“Miliyan 2.7, hukumar da ake biyan 540k, 80k duk wata gaba daya jimillar miliyan 4.2 kenan a shekara. Akalla 12k kenan a kullun. Ba kayan daki. Nawa ne dakin otel?"

Plantboyng ya ce:

"lol ta yaya kuke sa rana mai cin albashi zai karbi gida a irin wannan farashi mai ban tsoro? Gidan na da ka'ida kuma farshinsa yayi yawa. Tagogin sun yi kankanta, Kin cancanci fiye da haka."

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

Darlington Peters ya ce:

"wato bayan na biya kudin gidan sai kuma kudi kan kudi duk wata. baku fadi a ina kuke samun kudi ba."

042viktorchiya ce:

"miliyan 2.7 zai gina mun nawa gidan."

Abuja Ba Na Yaku-bayi Bane: Budurwa Ta Nuna Gidan Haya Na N750,000 Da Wani Dillali Ya Kaita, Bidiyon Ya Yadu

A wani labari makamancin wannan, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya, Tobi Oduns, ta shafe tsawon lokaci yanzu tana neman gidan haya a Abuja.

Budurwar wacce ke amfani da shafin TikTok tana ta yiwa mabiyanta a manhajar karin bayani game da yadda take faman neman gidan haya.

Kwanan nan ne wani dillalin gida ya dauke ta ya kaita wani gida mai daki daya wanda za a bayar da hayarsa kan N750,000 a babbar birnin tarayyar amma ko kadan bai burgeta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel