Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Saduwa Da Ni, Matar Aure Ta Fada Wa Kotu

Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Saduwa Da Ni, Matar Aure Ta Fada Wa Kotu

  • Wata Mata da ke neman a raba aurenta ta faɗa wa Kotu makasudin da yasa wasu lokutan take hana mijinta kwanciya da ita
  • Matar ta kai karar mijin gaban Kotun kostumare da ke Ibadan, jihar Oyo ne saboda tace tana rayuwar baƙin ciki da 'ya'yanta
  • Bayan sauraron kowane ɓangare, Alƙalin Kotun ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Satumba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo - Wata mata dake neman saki, Tawa Olayiwola, ranar Laraba, ta faɗa wa Kotun Kostumare da ke Ibadan, jihar Oyo cewa tana hana mijinta damar kwanciya da ita saboda tana zargin yana mata sata.

Misis Tawa, mahaifiyar ƴaƴa uku, ta shigar da ƙara gaban Kotun tana rokon Alkali ya datse igiyoyin aurenta da Olayiwola Ganiu, wanda suka shafe shakaru 19 tare.

Matar ta bayyana halin da take yanzu a cikin gidan aurenta da, "Rayuwar baƙin ciki," kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Suna Shirin Kashe Ni' Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Ya Aike da Sako Ga IGP, Ya Fallasa Sunaye

Shari'ar neman sakin Aure.
Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Saduwa Da Ni, Matar Aure Ta Fada Wa Kotu Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Da take wa Kotu jawabi, Tawa ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mai shari'a, wasu lokutan na kan hana Olayiwola damar yin jima'i da ni saboda yana ƙunsa mun bakin ciki a duk lokacin da ya sace mun wasu kayana. Duk lokacin da na hana shi sai ya kirani karuwa ko mara biyayya."
"Yana sace mun kadarori na da kuɗi a lokuta da dama tun ba yanzu ba kuma bai daina halin shi ba har yau. Duk da bai damu da kula da ƴaƴan mu ba, na siyo Talabijin amma ya sace shi."
"A takaice sai da na sanya aka cafke shi lokacin da ya ɗauke mun wayar salula, amma ya musanta cewa shi ya aikata."

A cewar matar, Mai gidanta bai taɓa nuna alamar sauke nauyin da ke kansa a matsayin uba ga ƴaƴan da suka haifa ba ko kuma matarsa, daily trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin kasa: 'Dan Uwan Budurwar da Shugaban Yan Bindiga Ke Kokarin Aurawa Kansa Ya Koka

Wane hali 'ya'yansu ke ciki?

Matar ta kuma yi ikirarin cewa Mijin ya ba ta N1,000 kuɗin cefane na tsawon watanni Shida. Ta jaddada cewa rashin sauke nauyin uba da ke kansa ya shafi babban ɗan mu.

"Halayensa ya shafi rayuwar babban ɗan mu na farko saboda yanzun yaron ya zama fitinanne a Anguwa. Mafi muni kuma, Olayiwola na lakada mun duka kan ƙaramin abu kuma zai iya komai kan duk wanda ya yi kokarin bani kariya."
"Ni ke ɗaukar nauyin biyan kuɗin hayar gidan da muke zaune, dan Allah a taimaka mun na dawo da kuɗi na."

A nashi ɓangaren, Mista Olayiwola Ganiu, bai yi musu kan bukatar mai ɗakinsa na neman saki ba. Ya roki Kotu ta raba auren amma ta ba shi ikon kula da ƴaƴan su.

Wane mataki Kotun ta ɗauka?

Alƙalin Kotun, mai shari'a S.M. Akintayo bayan sauraron kowane ɓangare, ya umarci ma'aurata su gabatar da ƴaƴansu a zama na gaba, daga nan ya ɗage zaman zuwa 30 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani Ɗan Jam'iyyar APC Ya Bindige Mutum Hudu a Babban Shagon 'Supermarket'

A wani labarin kuma Har yanzu sabo Fil nake, Bidiyon tsoho dan shekaru 90 wanda bai taba yin Budurwa ko Mata ba

Baizire Jean Marie ya kasance dan shekaru 90 wanda bai taba yin soyayya ba, haka bai haifi ‘ya’ya a waje ba.

Abun da ke ba mutane mamaki game da labarin mutumin shine cewa bai da wata matsala ta jiki ko kwakwalwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel