Abuja Ba Na Yaku-bayi Bane: Budurwa Ta Nuna Gidan Haya Na N750,000 Da Wani Dillali Ya Kaita, Bidiyon Ya Yadu

Abuja Ba Na Yaku-bayi Bane: Budurwa Ta Nuna Gidan Haya Na N750,000 Da Wani Dillali Ya Kaita, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna Tobi Oduns ta yada bidiyon gida da wani dallali ya kaita a Abuja
  • A cewar Tobi, mai gidan ya dage cewa lallai kan N750,000 zai bayar da hayar gidan duk shekara
  • Sai dai kuma, Tobi ta ce bata ji dadi ba bayan ta je ta ga gidan saboda palon ya yi kankanta fiye da tunaninta

Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya, Tobi Oduns, ta shafe tsawon lokaci yanzu tana neman gidan haya a Abuja.

Budurwar wacce ke amfani da shafin TikTok tana ta yiwa mabiyanta a manhajar karin bayani game da yadda take faman neman gidan haya.

Kwanan nan ne wani dillalin gida ya dauke ta ya kaita wani gida mai daki daya wanda za a bayar da hayarsa kan N750,000 a babbar birnin tarayyar amma ko kadan bai burgeta ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Magidanci Yayi wa Matashi Bayan Ya Ganshi Yana Tadin Mota da Budurwa

Budurwa, saurayi da gida
Abuja Ba Na Yaku-bayi Bane: Budurwa Ta Nuna Gidan Haya Na N750,000 Da Wani Dilalli Ya Kaita, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @tobioduns
Asali: UGC

Tobi ta ce ta bi dillalin zuwa gidan da nufin za ta ga wajen burgewa, amma abun bakin ciki shine bata ji dadi ba a yanayin da ta ga gidan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta, palon gidan ya yi kankanta sosai kuma wannan farashin sam bai yi ba a kan irin wannan gidan.

Kalamanta:

“Wannan shine waje na farko da na gani kuma daki daya ne sannan na ci buri sosai amma da na isa wajen, ban so yadda kankantar wajen yake ba musamman wajen palon. Ya yi kankanta da yawa. Kuma za a bayar da hayar wajen kan N750,000.”

Masu amfani da TikTok sun yi martani

@fawaz_egbon ya ce:

“Dubi yadda dilallin ke tafiya da fari, kamar zai kai ki wajen da kike mafarkin zuwa. Ya yi kankanta gaskiya, da fatan za ki ga wanda ya fi shi.”

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Budurwa Ta Gwangwaje Saurayinta da Kyautar PS5 Sabo Dal

@licia_brownnnyy ta yi martani:

“Wato idan bakina za su yi amfani da bandaki sai sun fara shiga dakina tukuna.”

@adanidet ya ce:

“Yanzu haka ina neman gida kuma zan iya cewa abun akwai zautarwa. Amma zan bi a hankali.”

@faridaberje ta yi martani:

“Nima ina shirin tashi don haka neman gida shine abun da nake yi kuma ba sauki ko kadan amma wadanda na gani na iyali 6 gaskiya ya yi.”

Kalli bidiyon a kasa:

"Na Kasance Talakar Karshe", Jarumar Fim Ta Magantu Kan Yadda Take Rokon Makwabta Abinci

A wani labarin kuma, Jarumar masana’antar shirya fina-finan kudu kuma tsohuwar yar gidan BBNaija, Bisola Aiyeola ta haddasa cece-kuce a tsakanin mutane da dama bayan ta magantu game da irin rayuwar da ta yi a baya.

Jarumar a cikin wani bidiyo da ya yadu ta bayyana yadda mutane suka cancanci duk wani abu da rayuwa ta kawo masu sannan cewa su karbi abun alkhairin da zai tunkaro su da hannu bibbiyu.

Kara karanta wannan

Kar yajin ya kare: Dalibin jami'a aji 3 ya kama sana'a, ya ce sana'arsa ya sa a gaba yanzu

Bisola ta bayyana cewa babu wata kyauta ta musamman ga mutumin da ya wahala yayin da ta sanar da mutane irin wahalar da ta sha a baya a rayuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel