Hukumar Shige Da Fice Zata Kara Daukar Sabbin Ma'aikata 5,000

Hukumar Shige Da Fice Zata Kara Daukar Sabbin Ma'aikata 5,000

  • Hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) ta ce nan ba da jimawa ba zata ɗauki sabbin jami'ai 5,000 a sassan Najeriya
  • Muƙaddashin shugaban hukumar, CG Idris Jere, ya ce sun tura wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bukatar ɗaukar ma'aikatan
  • CG ya je ta'aziyya ga iyalan jami'in NIS da ya rasu sakamakon harin yan bindiga a jihar Jigawa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Muƙaddashin shugaban hukumar shige ta fice ta ƙasa, (NIS), CG Idris Jere, ya ce shirye-shirye sun kankama na ƙara ɗaukar sabbin jami'ai 5,000 aiki.

Mista Jere, ya bayyana haka ne yayin zanta wa da manema labarai a Dutse Babban birnin jihar Jigawa. Ya ce zasu yi haka ne domin magance rashin isassun jami'ai a NIS.

Shugaban hukumar shige da fice NIS.
Hukumar Shige Da Fice Zata Kara Daukar Sabbin Ma'aikata 5,000 Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Premium Times ta ruwaito Idris Jere na cewa:

"Dangane da rashin isassun jami'ai a hukumar Shige da fice, kamar yadda kuka sani bamu jima da kammala ɗaukar ma'aikata ba kuma yanzu haka ana cigaba da aikin ba su horo ƙafin kama aiki."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Shugaban APC Na Jiha Ɗaya Ya Rasa Muƙaminsa, An Kore Shi Daga Jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Haka nan, kuna da sanin cewa gwamnati ta sanya takunkumi a fannin ɗaukar ma'aikata, amma ta ɗaga wa hukumomin tsaro kafa, saboda tsaro shi ne makullin komai."
"Saboda haka mun rubuta wa shugaban ƙasa takarda kuma ina da yaƙinin zamu samu amincewarsa na ɗaukar sabbin ma'aikata 5,000 a hukumar NIS."

Bugu da ƙari, ya bayyana cewa Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya tura kundin bukatar ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya nuna ƙarara cewa zai amince da ita.

Meya kai shugaban NIS jihar Jigawa?

Shugaban hukumar NIS ya kai ziyara Jigawa ne domin yin ta'aziyya ga iyalan ɗaya daga cikin jami'an hukumar da yan bindiga suka kashe ranar 9 ga watan Agusta da kuma gaida waɗan da ke kwance a Asibiti.

Mamacin na aiki a ɗaya daga cikin sansanin hukumar Shige da fice a hanyar Birniwa-Galadi, ƙaramar hukumar Birnawa a jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Ƙasa Buhari Ya Dira Babban Birnin Jihar Borno, Hotuna Sun Bayyana

Yan bindiga sun buɗe wa jami'an wuta ne suna tsaka da aikin Sintiri, wanda ya yi sandin rasuwar ɗaya daga cikin su, Abdullahi Mohammed (CIA), yayin da wasu biyu suka ji muggan raunukan harbi.

CG ya jaddada cewa hukumar ba zata yi ƙasa a guiwa ba a kokarin da take na tabbatar da tsaro a iyakokin Najeriya, kamar yadda This Day ta ruwaito.

A wani labarin kuma Yan sanda sun fito zanga-zanga kan rashin biyan su Albashi sama da Watanni 15 a Jihar Kwara

Kuratan yan sanda a jihar Kwara sun gudanar da zanga-zanga kan rashin biyan su Albashi tsawon watanni 16.

Yayin zanga-zangar su, yan sandan sun mamaye muhimman wurare ciki har da titin zuwa fadar gwamnatin jiha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel