AIT, Silverbird Da Sauran Tashoshin Watsa Labarai 50 Da Gwamnatin Najeriya Ta Rufe
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta rufe tashohin watsa labarai fiye da 50 a kasar saboda laifin kin sabunta lasisin aikinsu
- Tashohin da abin ya shafa sun hada da gidan talabijin na Silverbird, tashar AIT da Raypower FM, Rhythm FM da sauransu
- Balarabe Shehu Ilelah, shugaban hukumar NBC ya ce za a bawa tashoshin wa'adin kwana 30 su sabunta lasisinsu idan ba haka ba hukunci ya hau kansu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Hukumar kula da kafafen watsa labarai ta kasa, NBC, ta kwace lasisin kafafen watsa labarai na Silverbird TV, AIT, Raypower FM, Rythm FM da wasu saboda rashin sabunta lasisin aikinsu, Daily Trust ta rahoto.
Direkta Janar na NBC Mallam Balarabe Shehu Ilelah kuma ya umurci ofisoshinsu na jihohi su yi aiki tare da jami'an tsaro domin tabbatar da cewa an rufe kafafen watsa labaran cikin awa 24.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnatin na bin tashoshin kudi har Naira Biliyan 2.66 a cewarsa.
Mataimakin shugaban kasa Buhari na masamman a bangaren sabon fasawar watsa labarai, Bashir Ahmad shima ya tabbatar da umurnin rufe tashoshin watsa labaran a shafinsa na Twitter.
A cewarsa, a watan Mayu, hukumar ta wallafa sunayen tashoshin da ba su riga sun sabunta lasisinsu ba aka kuma basu sati biyu idan ba aka ba a kwace lasisin.
Ya ce watanni uku bayan fitar da sanarwar, wasu tashoshin ba su biya bashin da ake binsu ba hakan kuma ya saba dokar Act CAP N11, ta Tarayyar Najeriya, 2004, musamman sashi na 10(a) na sashi na uku na dokar.
Da ya ke sanar da janye lasisin, Ilelah ya bawa tashoshin da abin ya sha awa 24 su rufe.
Gwamnati ta bawa tashoshin wa'adin kwana 30 su sabunta lasisinsu
Ya yi kira ga dukkan tashohin da abin ya shafa su sabunta lasisinsu cikin kwana 30 don gudun kada a hukunta su.
Ya yi kira da dukkan tashoshin da ke watsa shirye-shiryensu ta intanet su yi rajista da hukumar don kada a katse su.
Ya ce ko sun biya bashin da ake binsu, sai sun biya wani kudin cigaba da watsa labarai.
Ga jerin tashoshin da abin ya shafa:
- Silverbird TV (Silverbird Communications Co. Ltd) Network
- Rhythm FM (Silverbird Communications Ltd)
- AIT/Ray Power FM (DAAR Communication Ltd)
- Greetings FM (Greetings Media Ltd)
- Tao FM (Ovidi Communications Ltd)
- Zuma FM (Zuma FM Ltd)
- Crowther FM (Crowther Communications Ltd)
- We FM (Kings Broadcasting Ltd)
- Linksman International ltd
- Bomay Broadcasting Services Itd
- MITV (Murhi International Group Ltd)
- Classic FM (Pinkt Nigeria Ltd)
- Classic TV (Pinkt Nigeria Ltd)
- Beat FM (Megalectrics LTD)
- Cooper Communications Itd
- Splash FM (West Midlands Ltd)
- Rock City FM (Boot Communications Itd)
- Family FM (Kalaks Investments Nig. Ltd)
- Space FM (Creazioni Nig. Ltd)
- Radio Jeremi (Radio Jeremi Ltd)
- FM Abuja
- FM Lagos
- FM Yenagoa
- FM Port-Harcourt
- FM Jos
- Wave FM (South Atlantic Media Ltd)
- Kogi State Broadcasting Corporation
- Kwara State Broadcasting Corporation
- Niger State Broadcasting Corporation
- Benin Network
- FM Network
- FM Okene
- FM Suleja
- FM Abuja
- FM Benin
- Breeze FM (Bays Water ltd)
- Vibes FM (Vibes Communication Itd)
- Family Love FM (Multimesh Broadcasting Co. Ltd) Port-Harcourt
- FPort-Harcourt
- Gombe State Broadcasting Corporation
- Lagos DSB
- Lagos State Broadcasting Corporation
- Osun State Broadcasting Corporation
- Ogun State Broadcasting Corporation
- Ondo State Broadcasting Corporation
- Rivers State Broadcasting Corporation
- Bayelsa State Broadcasting Corporation
- Cross River State Broadcasting Corporation
- Imo State Broadcasting Corporation
- Anambra State Broadcasting Corporation
- Borno State Broadcasting Corporation
- Yobe State Broadcasting Corporation
- Sokoto State Broadcasting Corporation
- Zamfara State Broadcasting Corporation
- Kebbi State Broadcasting Corporation
- Jigawa State Broadcasting Corporation
- Kaduna State Broadcasting Corporation
- Katsina State Broadcasting Corporation
Asali: Legit.ng