Zan Gyara Fannin Ilimi Cikin Watanni 6 Idan Aka Zabe Ni, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar Accord

Zan Gyara Fannin Ilimi Cikin Watanni 6 Idan Aka Zabe Ni, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar Accord

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Accord ya magantu, ya ce shi ke makulin gyara fannin ilimi a Najeriya
  • Farfesa Chris Imumolen ya ce idan aka zabe shi a 2023 zai gyara fannin ilimi a Najeriya cikin kasa da watanni shida
  • A halin yanzu, kungiyar malaman jami'o'i na ta yajin aiki, sun shafe sama da watanni shida makarantu na garkame

Jihar Legas - Farfesa Chris Imumolen, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Accord, ya sha alwashin gyara fannin ilimin Najeriya cikin watanni shida idan aka zabe shi a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Imumolen, dan takara mafi karancin shekaru a jerin 'yan takarar shugabancin Najeriya a halin yanzu, ya yi wannan alkawarin ne yayin wani gagarumin taron tattaunawa da kungiyar PCI ta shirya a Legas.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ya kamata daliban jami'a su maka ASUU a kotu, su nemi diyyar bata lokaci

Dan takarar shugaban kasa ya yi alkawarin gyara ilimi a Najeriua cikin wata shida
Zan Gyara Fannin Ilimi Cikin Watanni 6 Idan Kuka Zabe Ni, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar Accord | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A taron ya kuma kaddamar da wasu tsare-tsare na karfafawa manoma da sauran masu sana’o’i don ba su kwarin gwiwa da habak kasuwanci da noma a kasar.

A wannan taron ne dai har ila yau ya fitar da kudade, miliyoyi da yawa ga mutane daban-daban.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Imumolen, zuba jari a kan dan Adam shi ne abu mafi mahimmanci, dalilin da ya sa ya yi alkawarin ba ta kulawa a musamman a fannin kenan matsayinsa na shugaban kasa.

Ya kuma jaddada cewa za a ware 20% cikin 100% a matsayin kasafin kudin fannin ilimi don tabbatar da cewa abubuwa sun yi kyau sosai, rahoton Vanguard.

Ya kuma ba da tabbacin cewa fannin ababen more rayuwa za su samu kaso mai tsoka ta hanyar yin kwaskwarima ga tsarin da zai kawar da cin hanci da rashawa da suka dabaibaye muhimmin bangarori a Najeriya na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Goro a miya: Gwamnoni sun taru a Aso Rock don tattauna batun tattalin arziki, Buhari bai halarta ba

A cewarsa:

“Idan na zama shugaban Tarayyar Najeriya, zan tabbatar da cewa za a biya malamai albashi yadda ya kamata; kuma za a inganta wuraren karatu ga dukkan dalibai, kuma za su sami daidaiton al'adu tare da daliban kasashen waje kamar dai turawa tare da dalibai daga sassa daban-daban da za su ga fannin ilimin Najeriya ya burge su sosai."

Ya Zama Dole ASUU Ta Biya Diyya Ga Daliban da Suka Batawa Lokaci, inji Minista Adamu

A wani labarin, ministan Ilimi a Najeriya, Adamu Adamu, a ranar Alhamis, ya ce alhakin kungiyar malaman jami’o’i ne ta biya daliban jami'a diyyar lokacin da suka bata yayin yajin aikin na watanni shida na ASUU ba gwamnatin tarayya ba.

Ya kuma ce gwamnati ba za ta amince da bukatar kungiyar na biyan malamai kudaden alawus-alawus din su na tsawon watanni shida da suka bata ba tare da aikin karantarwa ba, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

Adamu ya ba da shawarar cewa daliban da abin ya shafa su kai ASUU kotu domin neman diyya bisa lokacin da kungiyar ta bata musu yayin yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel