Yan Bindigan Da Suka Sace Kwamishinan Nasarawa Sun Rage Yawan Kudin Fansa

Yan Bindigan Da Suka Sace Kwamishinan Nasarawa Sun Rage Yawan Kudin Fansa

  • Masu garkuwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Nasarawa, Lawal Yakubu, sun rage yawan kudin fansa
  • A wata waya da suka kira yau Alhamis, yan bindigan sun nemi miliyan N20m maimakon miliyan N100m da suka bukata tun farko
  • Kakakin yan sanda ya ce dakarun hukumarsu, sojoji, yan banga da mafarauta sun mamaye baki ɗaya yankin don ceto kwamishinan

Nasarawa - Yan bindigan da suka yi garkuwa da kwamishinan yaɗa labarai, al'adu da yawon buɗe ido na jihar Nasarawa, Lawal Yakubu, sun rage yawan kuɗin fansa zuwa miliyan N20m.

Daily Trust ta tattaro cewa yan bindiga sun yi awon gaba da kwamishinan ne a gidansa da ke Nasarawa Eggon, hedkwatar karamar hukumar Nasarawa Eggon ranar Litinin.

Taswirar jihar Nasarawa.
Yan Bindigan Da Suka Sace Kwamishinan Nasarawa Sun Rage Yawan Kudin Fansa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa an ƙara tura dakaru na musamman daga Barikin Doma, hedkwatar ƙaramar hukumar Doma, jihar Nasarawa zuwa yankin Nasarawa-Eggon.

Kara karanta wannan

Na Yi Alkawarin Kuɗi N50,000 Ga Duk Wanda Ya Fallasa Bayanan Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan APC

Wani ɗan gidan su kwamishinan, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya faɗa wa yan jarida cewa masu garkuwan sun sake kiran waya yau Alhamis da ƙarfe 10:30 na safe suka buƙaci miliyan N20m.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewa iyalan kwamishinan sun yi wa yan bindigan tayin miliyan N4.5m, amma suka yi watsi da adadin kuɗin kana suka gimtse wayar su cikin fushi.

A kalamansa ya ce, "Masu garkuwan sun sake kiran waya da ƙarfe 10:30 na safiyar yau Alhamis kuma suka zabtare kuɗin fansar daga miliyan N100m zuwa N20 miliyan."

Wane matakai hukumomi ke ɗauka?

A baya-bayan nan, gwamna Abdullahi Sule ya umarci a garkame baki ɗaya makarantun da ke faɗin sassan kananan hukumomi 13 na jihar Nasarawa bayan hukumomin tsaro sun tattara wasu bayanan sirri.

A halin yanzun, kakakin yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel, ya ce gamayyar yan sanda, sojoji, yan banga har da mafarauta sun mamaye yankin da nufin ceto kwamishina, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace kwamishina a Arewa, suna neman fansa N100m

A wani labarin kuma 'Ladan N50,000' Gwamnan APC Ya Bullo da Sabuwar Hanyar Yaƙi da Yan Bindiga a Jiharsa

Gwamnan jihar Ondo ya ware ladan N50,000 ga duk mutumin da ya taimaka da bayanai aka kama ɗan ta'adda a jihar.

Jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa, gwamna Oluwarotimi Akeredolu, ya ce gwamnati ta shirya kawo karshen yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel