Duk Wanda Ya Fallasa Bayanan Yan Bindiga Zamu Ba Shi Ladan N50,000, Gwamnan Ondo

Duk Wanda Ya Fallasa Bayanan Yan Bindiga Zamu Ba Shi Ladan N50,000, Gwamnan Ondo

  • Gwamnan jihar Ondo ya ware ladan N50,000 ga duk mutumin da ya taimaka da bayanai aka kama ɗan ta'adda a jihar
  • Jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa, gwamna Oluwarotimi Akeredolu, ya ce gwamnati ta shirya kawo karshen yan bindiga
  • Gwamnan ya kirkiro da sabon lamarin ne a kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'umma

Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya yi alƙawarin cewa zai ba da ladan N50,000 ga duk wanda ya fallasa bayanai da suka yi sanadin kama masu garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka.

The Nation ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kai, Misis Bamidele Ademola-Olateju, jim kaɗan baya taron majalisar zartaswa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani Ɗan Jam'iyyar APC Ya Bindige Mutum Hudu a Babban Shagon 'Supermarket'

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo.
Duk Wanda Ya Fallasa Bayanan Yan Bindiga Zamu Ba Shi Ladan N50,000, Gwamnan Ondo Hoto: @Thenationnews
Asali: UGC

Ya ce gwamnati ta ɓullo da wannan tsarin ne da nufin ƙara wa mutane kwarin guiwa su riƙa fallasa bayanai a lokacin da ya dace game da abinda ya shafi ayyukan yan ta'adda a sassan jihar.

Gwamnan ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Daga yanzu, duk wanda ya kawo rahoton aikata babban laifi kuma muka bi diddigi har muka samu nasarar hukunta masu laifin, wannan mutumin zai samu ladan N50,000."
"Muna son mutane su cire tsoro su yi magana idan suka ga wani abu ya faru. Muna son mutanen mu su tashi tsaye a fannin tsaro, ta yadda zamu magance yan bindigan jihar Ondo, yan ta'adda da sauran su."
"Kowa na da damar amfani da Lambar da ka ware, ya kira domin ba da bayanan tsaro ko ya miƙa rahoton aikata wasu manyan laifuka a yankinsa ko yankinta."

Kara karanta wannan

Luguden Wuta: Sojoji Sun Hallaka Ƙasurguman Yan Ta'adda da Yawa a Yankuna Uku Na Arewa

Ya ƙara da cewa gwamnati a shirye take ta ba da kariya ga duk wanda ya fito ya ba da rahoto ko wasu bayanan sirrin ayyukan ta'addanci a yankinsa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ɗan Daban APC ya harbe mutum huɗu a Ondo

A wani labarin kuma Wani Dan Daban Siyasa Ya Bindige Mutum Hudu a Cikin Kasuwa a Jihar Ondo

Wani mutumi da ake tsammanin ɗan daban siyasa ne ya bindige mutum huɗu a babban shagon Super Market a jihar Ondo.

Ɗan daban wanda ake wa laƙabi da, Para, ɗan APC, ya yi kaurin suna wajen yi wa mutane kwace ta dole a yankin karamar hukumar Idanre.

Asali: Legit.ng

Online view pixel