Buhari ya Sabunta Nadin Shugaban Hukumar DSS mai Shekaru 66, An Gano Dalili
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta nadin Yusuf Bichi matsayin shugaban hukumar tsaro ta farin kaya
- Majiya daga fadar shugaban kasa ta tabbatar, Buhari ya yi hakan ne domin Bicihi ya dasa daga inda yake niyyar tsayawa wurin aiki tukuru a hukumar
- An mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari sunayen mutane daban-daban wadanda zasu iya maye gurbin Bichi amma duk yayi watsi da su
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsawaita wa'adin darakta janar na hukumar tsaron farin kaya, Yusuf Bichi, Daily Nigerian ta ruwaito.
Bichi ya fara shugabantar hukumar hukumar a watan Satumban 2018 bayan ritayar Matthew Seiyefa, wanda ya jagoranci hukumar sirrin a matsayin mukaddashin shugaba daga 7 ga watan Augustan 2018 zuwa 14 ga watan Satumban 2018.
A yayin tabbatar da wannan cigaban ga Daily Nigerian, kakakin hukumar tsaron farin kayan, Nnochirionye Afunanya, yace "an sabunta wa'adin mulkin darakta janar din."
Majiyar cikin gida ta sanar da Daily Nigerian cewa lokacin da wa'adin mulkin Bichi ya karato, an mika sunayen wasu wadanda zasu iya maye gurbinsa amma shugaban kasan bai karba ko daya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda majiyoyi suka sanar daga fadar shugaban kasa, shugaban kasan ya so Bichi ya cigaba da aikin kirkin da yake yi wurin tattaro bayanan sirri a maimakon nada sabon hannu da zai fara daga tushe.
Bichi mai shekaru 66 ya halarci sakandaren Danbatta, kwalejin ilimi na Kano da jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria inda ya kammala digirinsa a fannin siyasa.
Ya fara aikinsa a matsayin jami'i a jihar Kano, daga nan ya shiga tsohuwar hukumar tsaro ta Najeriya, NSO, kafin ta zama hukumar SSS ta yanzu.
Shugaban kasa Muhammadu ya sake kiransa a watan Satumban 2018 bayan yayi ritaya daga aiki da shekaru biyu domin ya zama darakta janar na hukumar.
Batan N431m: Yadda Magu ya Wuwushi Kudi, Ya Biya Kudin Lantarkin Gidan Gonarsa
A wani labari na daban, kwamitin bincikar Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da almundahana da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, yace ba zai iya bayyana yadda aka kashe N431 miliyan ba na tsaro da aka warewa ofishin Magu ba tsakanin 2015 zuwa 2020.
A rahoton karshe da aka mikawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Nuwamban 2020, an gano cewa Magu yayi amfani da wasu daga cikin kudin wurin biyan kudin wutan gonarsa dake Karshi Development Area dake Nasarawa, TheCable ta rahoto.
Asali: Legit.ng