Batan N431m: Yadda Magu ya Wuwushi Kudi, Ya Biya Kudin Lantarkin Gidan Gonarsa

Batan N431m: Yadda Magu ya Wuwushi Kudi, Ya Biya Kudin Lantarkin Gidan Gonarsa

  • Kwamitin Mai Shari'a Ayo Salami ya bankado yadda Ibrahim Magu, dakataccen shugaban EFCC ya handama daga cikin N431 miliyan ya biya wutar lantarkin gidan gonarsa
  • Kamar yadda rahoton binciken Magun da aka mika ofishin sakataren tarayya ya bayyana, ya kwasa daga kudin inda ya biya kudin kallon talabijin na gidansa dake Karu
  • A yayin da aka tuntubi lauyan Ibrahim Magu, ya ki tofa albarkacin bakinsa kan zancen inda yace har a halin yanzu bai samu ganin takardun binciken da kwamitin Salami yayi ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Kwamitin bincikar Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da almundahana da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, yace ba zai iya bayyana yadda aka kashe N431 miliyan ba na tsaro da aka warewa ofishin Magu ba tsakanin 2015 zuwa 2020.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa IBB ya rigamu gidan gaskiya

A rahoton karshe da aka mikawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Nuwamban 2020, an gano cewa Magu yayi amfani da wasu daga cikin kudin wurin biyan kudin wutan gonarsa dake Karshi Development Area dake Nasarawa, TheCable ta rahoto.

Ibrahim Magu
Batan N431m: Yadda Magu ya Wuwushi Kudi, Ya bIya Lantarkin Gidan Gonarsa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kwamitin ya kara da cewa, tsohon shugaban EFCC yayi amfani da wani bangare na kudin wurin biyan kudin kallon talabijin na gidansa dake yankin Karu a jihar.

Kwamitin da ya samu shugabancin Ayo Salami, tsohon babban alkalin kotun daukaka kara, an kafa shi ne domin binciken Magu tun daga watan Mayun 2015 zuwa Mayun 2020, lokacin da ya mulki hukumar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

TheCable ta gano an mika rahoton zuwa ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Lokacin da TheCable ta tuntubi lauyan Magu, Wahab Shittu domin yayi martani kan lamarin, ya ki cewa komai saboda yace bai ga takardun ba.

Kara karanta wannan

Karon Farko a Tarihi, Buhari Ya Kirkiro Sabon Mukami Domin Magance Rashin Tsaro

Ku Nemi Taimakon Ubangiji Kan Al'amuran Siyasarmu, IBB Ga 'Yan Najeriya

A wani labari na daban, Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, yace 'yan Najeriya su nemi taimakon Ubangiji kan alkiblar da zasu dosa a al'amuran siyasar kasar nan.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Babangida ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Niger domin tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa.

Tsohon shugaban kasan ya cika shekaru 81 a ranar 17 ga watan Augustan 2022. A jawabinsa, yayi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da yin imani wurin hadin kan kasar nan tare da mayar da hankali da sa ran cewa komai zai daidaita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel