'Yan Majalisa Sun Gayyaci Ministar Kudi, Suna Neman Takardun Tallafin Man Fetur

'Yan Majalisa Sun Gayyaci Ministar Kudi, Suna Neman Takardun Tallafin Man Fetur

  • Majalisar wakilai a Najeriya ta gayyaci ministar kudi domin tattauna wasu batutuwa da suka shafi kudin 'yan Najeriya
  • A makwannin da suka gabata ne aka ce gwamnatin Najeriya za ta ware makudan biliyoyi da sunan tallafin man fetur
  • Har yanzu, Najeriya, kasa mai arzikin man fetur bata kubuta da tsada da karancin man fetur ba duk da akwai shi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta gayyaci ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Hajiya Zainab Ahmed domin ta gabatar da dukkan takardun da suka shafi batun tallafin mai daga 2013 zuwa yau.

Ibrahim Aliyu, shugaban kwamitin wucin gadi na musamman da ke binciken tsarin tallafin man fetur ne ya bayyana hakan a lokacin da Stephen Okon, Daraktan kudi na cikin gida a ma’aikatar ya bayyana a gabansa a Abuja ranar Talata.

Kara karanta wannan

Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

Shugaban kwamitin ya baiwa ministar zuwa ranar 16 ga watan Agusta ta kawo kanta da duk wasu takardun da suka dace a ikirarin tallafin man fetur, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ana neman ministar kudi game da kudaden tallafin man fetur
'Yan Majalisa Sun Gayyaci Ministar Kudi, Suna Neman Takardun Tallafin Man Fetur | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shugaban ya ce dole ne ministar ta amsa tambayoy kan jimillar kudaden da aka fitar daga asusun ajiyar kudaden shiga a matsayin na tallafin mai daga 2013 zuwa yau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce dole ne a gabatar da bayanan kamfanonin da suka ci gajiyar kudaden tallafin daga asusun tattara kudaden shiga.

A cewar shugaban, furucin da ministar ta yi kwanan nan na cewa kasar za ta bukaci Naira tiriliyan 6.7 na tallafin man fetur abin damuwa ne ainun.

Ya ce ya zama wajibi ministar ta gurfana a gaban kwamitin domin bayyana wasu batutuwa, inda ya ce tun da za a aro kudin tallafin ne domin 'yan Najeriya su mora.

Kara karanta wannan

Sai Da Na Gargadi Buhari Cewa Zai Lalata Kasar Nan - Khalifa Sanusi

Ya kara da cewa, batun lamari ne mai tsanani da ke bukatar tsoma bakin kowa da kowa, ya kara da cewa kwamitin na rike amana ne na ‘yan kasa.

Mista Okon, ya ce dole tasa ya bayyana saboda ma’aikatar ba ta son fitar bayanan da ba a aiwatar da su yadda ya kamata ba a gaban kwamitin, inji rahoton The Guardian.

Ya ce ya zo ne domin neman a kara masa lokaci, inda ya ce ba shi da hurumin gabatar da komai a gaban kwamitin.

Ya ce ma’aikatar za ta so ta nemi karin lokaci don tattara bayanan da ake bukata kafin zuwa gaban kwamitin.

Gwamnatin Buhari za ta kashe N6.72trn a matsayin tallafin man fetur a 2023

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta ce za ta tanadi kudaden tallafin man fetur a shekarar 2023 da akalla za su kai sama da Naira tiriliyan 6.72.

Ministar Kudi ta Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis yayin taron kashe kudade na 2023 – 2025 na MTEF da FSP, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

Zainab Ahmed ta ce gwamnati ta yi hasashen sakamakon kasafin kudi matsakaici ta fuska da yanayi biyu dangane da ma'auni na kasafin kudin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel