Ba Zamu Iya Ciwo bashin N1.1trn don kawo karshen yajin aikin ASUU ba, Ministan Kwadago

Ba Zamu Iya Ciwo bashin N1.1trn don kawo karshen yajin aikin ASUU ba, Ministan Kwadago

  • Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta iya ciwo bashin Triliyan N1.1trn a duk shekara don warware matsalar ASUU ba
  • Ministan Kwadago ya nemi kungiyar ASUU su janye yajin aiki saboda basu kadai bane hukumar dake ci daga Asusun gwamnatin Najeriya ba
  • Festus Keyamu ya bukaci iyayen dalibai a fadin kasar su roki kungiyar ASUU ta bar malamai su koma bakin aikin su

Abuja - Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, ya bayyana a jiya cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da hurumin ciyo bashin Naira Tiriliyan 1.2 a duk shekara domin warware yajin aikin da kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) su ka shiga. Rahoton THE NATION

Martanin Festus Keyamo kenan a lokacin da yake amsa tambayoyi a gidan talabijin na Channels TV.

Kara karanta wannan

Har gara 2015: Kasar nan na cikin ha’ula’i, ba a ga komai ba sai 2023 inji Sanusi II

Keyamu yace matsin lamba kungiyar ASUU ba zata sa gwamnati ta ciyo bashin Naira Tiriliyan 1.2 dan biyan bukatun ta ba, wanda idan aka yi la’akari adadin kudin shiga da kasar ke samu, bai wuce Naira Tiriliyan 6.1 a lokacin da muke da hanyoyin, cibiyoyin kiwon lafiya da za mu gina, ga kuma sauran fannoni da ke bukatar kulawa a kasar.

Keyamo
Gwamnatin Tarayya ba za ta iya ciwo bashin Triliyan N1.1trn don kawo karshen yajin aikin ASUU ba – Keyamo FOTO The Nation
Asali: Twitter

Daga nan Festus Keyamu ya bukaci iyaye a fadin kasar da su rika rokon kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da take yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Keyamu yace, yakamata su koma bakin aikin su, saboda basu kadai bane hukumar dake ci daga asusun Najeriya ba, Najeriya baza ta tsaya cak saboda an kasa biyan bukatun ASUU ba.

Sojoji Sun Kashe Wani Dansanda Bayan Sun Lakada Mishi Dukan Tsiya A Legas

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro : NSCDC Ta Yiwa Iyalan Jami'inta Da Aka Kashe Kyauta Mai Tsoka

A wani labari kuma, Wasu fusatattun sojoji sun lakada wa wani dan sanda duka inda suka kashe har lahira a wani hari da suka kai kan babbar hanyar Mile 2 Badagry a jihar Legas a ranar Laraba. Rahoton Daily Trust

Dan sandan da ya rasu ya kasance Insifeto ne da ke aiki da sashen Ojo na rundunar ‘yan sandan jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel