Bidiyon Shigowar Kasaita Da Amarya Amina Isiyaka Rabiu Tayi A Wajen Liyafar Aurenta
- Komai idan aka ce na manya ne ya kan zo da sabon salo da ba a saba gani ba, harma ka ga ya zama abun kwaikwayo a cikin mutane
- Amina Isiyaka Rabiu ta yi wani kasaitaccen bayyana a wajen liyafar bikinta da angonta Muhammad Shehu Rabiu
- A cikin bidiyon shahalin wanda tuni ya yadu a soshiyal midiya, an gano amaryar tafe a cikin wani abun daukar amare da aka kera don ita
Ana ta daure-dauren aure na ‘ya’yan manya a fadin kasar inda a wannan makon shagalin ya fada a kan yar mutan Kano.
A yanzu haka ana nan ana gudanar da shagulgulan bikin Amina Isiyaka Rabiu da angonta Muhammad Shehu Rabiu.
Tuni bidiyon kasaitaccen liyafa na musamman da aka shiryawa sabbin ma’auratan ya yadu a shafukan soshiyal midiya.
A cikin wani bidiyo da shahararriyar MC nan ta Arewa wacce ake yayi a yanzu, Surrykmata ta wallafa a shafinta na Instagram, an gano lokacin da amarya Amina ta shigo dakin taron.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai sabanin yadda aka saba inda kawaye ke yiwa amarya rakiya, Amina ta shigo ne a cikin wani abun dauka yayin da wata tawaga ta musamman ke rike da abun.
An kuma gano amaryar a tsakiyar abun wanda aka kera shi kamar gida tana tafiyar kasaita zuwa wajen da aka tanada domin zamanta da angon nata.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
neelah_elegance ta ce:
"Ikon Allah"
mum_albanys_kitchenworld ta rubuta:
"Kai jamaaa anty barni in yi magana ana abu aduniya"
sumeebelels_cuisine ta ce:
"Tohm bakina alekum, nidei dan tambaya zan yi dama"
shopers_delight_kn ta ce:
"In da ranka ka sha kallo"
its_teamerh ta yi martani:
"Wannan shine namu ba irin nasu bane"
Zukekiyar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero Za Ta Shiga Daga Ciki
A wani labarin kuma, mun ji cewa Ruqayya Aminu Bayero, kyakkyawar diyar sarkin Kano, Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, na shirin amarcewa da angonta.
Za a kulla aure tsakanin Rukayya da angonta Amir Kibiya a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba mai kamawa a fadar mai martaba Sarkin Kano.
Tuni katin gayyatar auren ya bayyana a shafukan soshiyal midiya kuma shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram.
Asali: Legit.ng