Bidiyon Yadda Amarya Ta Zage Ta Kwashi Garar Girki Kafin Ta Shiga Filin Rawa

Bidiyon Yadda Amarya Ta Zage Ta Kwashi Garar Girki Kafin Ta Shiga Filin Rawa

  • Kamar yadda aka saba idan ana bikin aure ba a fiye damuwa da tabbatar da ko amare sun ci abinci ba kawai dai su shirya su je wajen shagali shi aka fi ba muhimmanci
  • Wata amarya ta yiwa kanta kiyamul laili inda ta nemi abinci ta take cikinta kafin ta samu karfin shiga filin rawa
  • Bidiyon wanda ya yadu a shafukan soshiyal midiya sun sanya mutane tofa albarkacin bakunansu, da dama sun goyi bayan matakin da amaryar ta dauka

Yawanci idan ana shagulgulan aure ba a damu da baiwa amare abinci ba a wannan rana ganin cewa saboda su ne aka tara jama’a.

Hankula sun fi karkata wajen tabbatar da ganin baki da aka gayyata sun ci sun sha yadda ya kamata.

Wasu har sai ka ga amaren sun jigata basu da wani kuzari saboda ciki bai dauka ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

Sai dai wata amarya ta sauya wannan al’ada inda aka haskota tana kwasar girki. An gano ango zaune a gefenta yayin da ita kuma take ta aika loman abinci.

Amarya da ango
Bidiyon Yadda Amarya Ta Zage Ta Kwashi Garar Girki Kafin Ta Shiga Filin Rawa Hoto: fabricblogger
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan ta take cikinta ta yi nak sai suka tashi suka garzaya filin rawa inda aka ci gaba da shagali tare da girgijewa.

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu a kan bidiyon wanda shafin fabricblogger na Instagram ya wallafa, wasu sun ce sam basu ga laifin amaryar ba gara da ta cika cikinta don samun karfi.

Kalli bidiyon a kasa:

Karanta martanin jama’a a kasa:

ubmeerat_treats ta yi martani:

"tama.kanta dibara."

aloydspeaker ta ce:

"Yasmine bata aiki kowa ba "

ummieyphatemerh_gwalabe ta ce:

"Ta burgeni "

zuzumamman ta rubuta:

"Ba za ta zo ta kashe kanta ba dan Allah "

fariha_ibrahim ta ce:

Kara karanta wannan

Bidiyo: Budurwa Ta Gane Cewa Mijinta Gurgu Ne Bayan Aurensu, Da Kafafun 'Acuci' Ya Dinga Zuwa Tadi

"Wlh da gaskiyan ta,haka aka barni da yunwa lokacin biki na. Kowa yaci ya goge baki amarya na fama da yunwa"

eemahaliyu ta ce:

"Wallahi amarya ci shinkahwa❤️"

ummeenerh ta ce:

"Nima ci zanyi"

Zukekiyar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero Za Ta Shiga Daga Ciki

A wani labarin kuma, Ruqayya Aminu Bayero, kyakkyawar diyar sarkin Kano, Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, na shirin amarcewa da angonta.

Za a kulla aure tsakanin Rukayya da angonta Amir Kibiya a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba mai kamawa a fadar mai martaba Sarkin Kano.

Tuni katin gayyatar auren ya bayyana a shafukan soshiyal midiya kuma shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel