Hukumar Yan Sanda Ta Ayyana Neman Wasu Mutum Biyu Ruwa a Jallo A Delta

Hukumar Yan Sanda Ta Ayyana Neman Wasu Mutum Biyu Ruwa a Jallo A Delta

  • Hukumar yan sanda ta bayyana neman wasu mutum biyu ruwa a jallo bisa zargin aikata ta'addanci a jihar Delta
  • Mai magana da yawun hukumar reshen jihar, DSP Bright Edafe, ya ce akwai kyauta mai tsoka da ke jiran duk wanda ya taimaka aka cafke su
  • Yan sanda na zargin Francis Odiakose da Christopher Odiakose, da yunkurin kisan kai, ta'addanci da wasu manyan laifuka

Delta - Hukumar yan sanda reshen jihar Delta ta ayyana neman Francis Odiakose da Christopher Odiakose, ruwa a jallo bisa zargin aikata ta'addanci, yunkurin kisan kai da wasu manyan laifuka..

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Warri, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Awanni Kaɗan Tsakani, Yan Bindiga Sun Sake Kai Wani Kazamin Hari Kusa Da Babban Birnin Jihar Katsina

Hukumar yan sanda.
Hukumar Yan Sanda Ta Ayyana Neman Wasu Mutum Biyu Ruwa a Jallo A Delta Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Edafe ya ƙara da cewa Kotun Majirtire da ke zamanta a Asaba, babbar Birnin Delta ce ta ba da umarnin damƙe waɗan da ake zargin a ko ina aka gan su.

Kakakin yan sandan ya kuma roki ɗaukacin mazauna jihar da sauran su da su yi ram da mutanen biyu duk inda suka gan su, kana suna damƙa su ofishin yan sanda mafi kusa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Neyasa ake neman su?

Mai magana da yawun yan sandan ya ce an yanke ayyana neman su ruwa a jallo ne kan Kes mai alaƙa da haɗin kai da ayyukan asiri.

Sanarwan ta ce:

"Hukumar yan sanda reshen jihar Delta na neman Francis Odiakose da Christopher Odiakose ruwa a jallo. Idan aka gan su, muna rokon al'umma Dan Allah a kama su kana a miƙa su Caji Ofis mafi kusa ko kuma su kai su Ofishin kwamishinan yan sanda."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Yan Arewa Mazauna Jihar Imo Tare da Filewa Mutum Daya Kai

Akwai kyauta ga wanda ya kama su - Yan sanda

Edafe ya ƙara da bayanin cewa mutane zasu iya tuntuɓar lambobin ofishin mai magana da yawun hukumar yan sanda ta 0915 557 0008 da 0915 557 0007.

"Kyauta mai tsoka na jiran duk wanda ya ba da wasu bayanai da zasu taimaka wajen cafke mutanen."

A wani labarin kuma Sojoji Sun Kai Samame Maɓoyar Yan Ta'adda, Sun Halaka Dandazon Su A Jihar Arewa

Rundunar Operation Haɗin Kai ta yi nasarar halaka dandazon mayaƙan Boko Haram a wani samame da ta kai sansanin su da ke Gazuwa.

Wata majiya ta bayyana cewa Soja ɗaya ya rasa rayuwarsa yayin gwabzawa, yayin da yan ta'adda da yawa suka zama gawa a yankin Bama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel