Bidiyo: Matasa sun je har gidan Sheikh Yabo don jinjina masa kan yadda yake cashe gwamnati

Bidiyo: Matasa sun je har gidan Sheikh Yabo don jinjina masa kan yadda yake cashe gwamnati

  • Matasan jihar Sokoto, sun yi tururuwa da yawansu har gidan Sheikh Bello Yabo domin jinjinawa tare da yaba masa
  • Kamar yadda bidiyo ya nuna, matasan sun sanar da cewa yadda yake fadin gaskiya ga gwamnati ne yasa suka je domin jinjina masa
  • Daga bisani malamin ya kwarara addu'o'i inda aka ji matasan suna amsawa da Amin sannan suna kabbara har ya wuce

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Bello Yabo na jihar Sokoto, ya samu gaisuwar ban girma da jinjina daga wasu matasa har gidansa.

Matasan da suka yi tururuwar zuwa gidan Shehin Malamin, sun bayyana cewa yadda yake fadawa gwamnati gaskiya ne yasa suka ce dole su je su yaba masa.

A bidiyon da aka nada na lokacin da matasan suka je gidan malamin, an gan shi tsaye yayin da matasan suka zagaye shi sun yaba masa yadda ya saka fadin gaskiya a gaba ga gwamnati a kan wannan rashin tsaro da yayi kamari.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Na Fadawa Tinubu Ban Bukatar Komai a Gwamnatinsa, Na Bada Dalilina

Sheikh Yabo da Buhari
Bidiyo: Matasa sun je har gidan Sheikh Yabo don jinjina masa kan yadda yake cashe gwamnati. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kamar yadda aka ji daya daga cikin matasan yana fadi:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tasowa muka yi muka ce zamu zo mu yaba maka."

Malamin yayi addu'o'i ga matasan inda suka dinga amsawa da Amin Malam.

Daga nan ya kutsa cikinsu inda ya fara tafiya suna biye da shi suna kabbara tare da cewa 'Sai Malam'.

Bidiyo: Buhari ka ci amanarmu, ko zuciyar Fir'auna gareka sai haka, Malam Bello Yabo

A wani labari na daban, fitaccen malamin nan na jihar Sokoto, Malam Bello Yabo, ya fito a sabon bidiyo yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari tatas kan yadda yayi watsi da lamarin fasinjojin jirgin kasa da ke hannun 'yan ta'adda.

A bidiyon da malamin ya saki a shafinsa na Facebook, ya sanar da cewa Buhari ya ci amanar 'yan Najeriya kuma Allah zai tuhumesa saboda rantsuwa da yayi da Qur'ani kan cewa zai yi adalci.

Kara karanta wannan

Har yanzu akwai harsashi a ciki na: Bidiyon labarin fasinjan jirgin Abd-Kad a hannun 'yan bindiga

Malamin ya kara da tambayar shugaban kasan idan da matarsa ko 'ya'yansa ne ke hannun 'yan ta'adda, haka zai nuna halin ko in kula?

Asali: Legit.ng

Online view pixel