An Baiwa Jami’in Karotan Da Ya Kama Manyan Motocin Giya, Tukuicin Naira Miliyan 1

An Baiwa Jami’in Karotan Da Ya Kama Manyan Motocin Giya, Tukuicin Naira Miliyan 1

  • Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta baiwa daya daga cikin jami’anta Halilu Jalo kyautar Naira miliyan 1 bisa kama motocin giya
  • Hukumar Karota ta ce an boye giya a cikin manyan motocin da aka yi wa lakabi da taliyar Indomie noodles
  • Mai magana da yawun hukumar karota, Nabulisi Abubakar ya ce gwamnatin jihar Kano ta hana zirga-zirga da shan barasa a fadin jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta baiwa daya daga cikin jami’anta Halilu Jalo kyautar Naira miliyan 1 bisa kama wasu manyan motoci guda biyu da giya a jihar. Rahoton Premium Times

Mista Jalo ya ki karbar cin hancin Naira 500,000 da aka ce mai barasa ya ba shi domin a sako motocin da aka kwace.

Kara karanta wannan

Kano Ta Amince Da Yiwa Daliban Jihar Karin Tallafin Alawus Da Kashi 50

Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa, Baffa Dan-Agundi, ya ce an kwace motar ne a ranar Alhamis a titin Obasanjo, cikin babban birnin Kano.

Karota
An Yiwa Jami’in Karotan Da Ya Kama Manyan Motocin Giya, Tukuicin Naira Miliyan 1 FOTO Daily Post
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar, Nabulisi Abubakar, da yake zantawa da manema labarai ya ce hukumar ta baiwa jami’in da ya kama manyan motocin naira miliyan daya bayan ya ki karba cin hancin N500,000 dan ya saki kayayyakin da aka kwace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mista Abubakar ya ce manyan motocin na dauke da akwatunan barasa sama da 2000 da kudinsu ya haura Naira miliyan 50.

An boye barasa a cikin manyan motocin da aka yi wa lakabi da taliyar Indomie noodles.

Abubakar yace gwamnatin jihar Kano ta hana zirga-zirga da shan barasa a fadin jihar.

Kungiyar KAROTA da ‘yar uwarta, Majalisar Kare Kayayyakin Ciniki ta Jihar Kano a karkashin jagorancinsa ba za ta kyale duk wanda aka kama ya shiga da kayan shaye-shaye cikin jihar ba.

Kara karanta wannan

A ina ta samo: Gwamnatin Buhari ta gano N500m a asusun malamar makarantan firamare, ta kwace

Ya yaba wa jami’in dan kishin kasa tare da jan hankalin sauran jama’a da su yi koyi da shi kuma a koda yaushe suna la’akari da tsaron rayuka da dukiyoyin jihar kafin komai.

Kano ta amince da karin kashi 50 na Kudin Tallafin Karatun Dalibai Marasa Galihu

A wani labar kuma, Majalisar zartaswar ta jihar Kano ta amince da karin kashi 50 cikin 100 na alawus din tallafin karatu ga dalibai ‘yan asalin jihar da ke halartar jami’o’in Najeriya. Rahoton TVC NEWS

Ta kuma ba da izinin sakin Naira miliyan 865.4 ga hukumar bayar da tallafin karatu ta jiha a matsayin alawus da ba a biya ba da kuma samar da kayan aiki na biyan dalibai a fadin kananan hukumomin jihar 44 dake masarautu biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel