A ina ta samo: Gwamnatin Buhari ta kame malamar makaranta da laifin mallakar N500m

A ina ta samo: Gwamnatin Buhari ta kame malamar makaranta da laifin mallakar N500m

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta sa wata malamar makarantar firamare ta yi asarar miliyoyin Nairori da aka gani a asusunta na banki
  • Hukumar ta ce ta gano jimillar Naira miliyan 540 a asusun malamar da albashinta bai zarce N76,000 ne kacal
  • A cewar hukumar ta ICPC, Egbuha ta yi aiki tare da wasu mutane da wani kamfani mai zaman kansa wajen karkatar da kudaden da aka samu bayan an kama ta

A ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC ta bayyana cewa ta gano jimillar Naira miliyan 540 a asusun wata malamar makarantar firamare na gwamnati mai karbar albashin N76,000.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta kuma bayar da umarnin a kwace Naira miliyan 120 na malamar, Roseline Egbuha da ke koyarwa a makarantar firamare ta Ozala, Abagana ta jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari na Shirin Kara Haraji, Farashin Yin Waya a Salula Zai Tashi

Yadda aka kwace kadarorin wata malamar makaranta
A ina ta samo: Gwamnatin Buhari ta kame malamar makarnta don ta mallaki N500m | Hoto: icpc.gov.ng
Asali: UGC

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Azuka Ogugua ya fitar ta ce kotun ta mai shari’a D.U Okorowo ta kuma bayar da umarnin a kwace motocin da aka gano Egbuha ta mallaka da wasu kayayyakinta da ake zargi na haramun ne.

Cikakken bayanin umarnin kotu akan Egbuha da sauran su

Ogugua ya bayyana cewa kotun ta bayar da umarnin ta a ranakun 26 da 27 ga watan Yuni amma lauyan hukumar ya samu ainihin takardun shaidar kadarorin ne a ranar Laraba 27 ga watan Yuli.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar ICPC, umarnin kotun ya biyo bayan karar da hukumar ta shigar ne a 2021.

Batun ya kuma biyo bayan zargin da aka yi na Naira miliyan 540 da ake alakantawa da Egbuha da wasu abokan harkallarta da suka yi yunkurin boye kudaden a asusunta na wani banki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Tallan Dankali Saboda Yajin Aikin ASUU

Matakin ICPC na yaki da cin hanci da rashawa

Binciken da hukumar ta yi ya kuma sa ICPC ta sanya aka daskarar da asusunta wanda hakan ya sa ta samu umarnin kotu daga babbar kotun tarayya da ke Abuja na dage daskararwar da aka sanya a asusun.

An tattaro cewa, bayan bude asusun, nan take wacce ake zargin ta cire kudaden kana ta tura su ga wasu asusu masu yawa mallakin 'yan canji da wasu mutane da suka hada da James Erebouye, Emon Okune da Chisom Iwueke.

Sauran sun hada da Alonge Ojo, Maureen Chidimma, Owoyemi Mayowa da Ejeaka Ifeoma baya ga wasu kamfanoni masu zaman kansu guda biyu da aka gurfanar da su a gaban kotu bisa laifukan damfara da kuma ajiyar kudaden da ake zargin na haramun ne.

Sauran abubuwan da aka kwace sun hada da motoci Toyota da Lexus da kuma wata Venza.

Kara karanta wannan

Duk sace N109bn na kasa, kotu ta ba da belin akanta janar da shugaba Buhari ya dakatar

Satar N109bn na kasa: Kotu ta ba da belin Akanta Janar da aka dakatar

A wani labarin, wata babbar kotun Abuja da ke zamanta a Maitama, a ranar Alhamis, ta ba da belin tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris.

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da kotu ta tasa keyar tsohon AGF din gidan yari, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A makon da ya gabata ne kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare Ahmed Idris da wadanda ake tuhuma tare dashi a gidan yari na Kuje har sai an saurari batun neman belinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.