An gano sabon na'uin sauro mai yada cutar maleriya a arewacin Najeriya, Cibiyar Bincike

An gano sabon na'uin sauro mai yada cutar maleriya a arewacin Najeriya, Cibiyar Bincike

  • Cibiyar bincke ta NIMR ta sanar da gano wani sabon nau'in sauro mai yada cutar maleriya a arewacin Najeriya
  • Kamar yadda darakta janar na cibiya, Farfesa Babatunde Salako ya bayyana, sunan sauron Anopheles Stephensi
  • Ya kwatanta sauron da gagararre wanda yake yada cuta maleriya mai tsananin hatsari kuma ba a taba ganin irinsa ba a Afrika ta yamma

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Cibiyar bincike ta najeriya ta NIMR ta bayyana cewa ta gano wani sabon nau'in sauro mai yada cutar maleriya mai suna Anopheles Stephensi a arewacin kasar Najeriya.

Darakta janar na cibiyar bincike, Farfesa Babatunde Salako ya sanar da manema labarai hakan a Legas yayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa karo na 63 a daren Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya tabbatarwa da manema labarai cewa, wannan yana daya daga cikin manyan abubuwan da suka gano a fanninsu.

Kara karanta wannan

Kamfanin Dubai Mai Ma’aikata 61,000 Ta Karrama Dan Najeriya A Matsayin Gwarzon Wata

Sauro
An gano sabon na'uin sauro mai yada cutar maleriya a arewacin Najeriya, Cibiyar Bincike. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda yace, nau'in sauron yana yada kwayar cutar maleriya mai suna plasmodium falciparum. Ya kwatanta sauron da gagararre wanda yake da wuyar ganin baya kuma ba a taba ganin irinsa ba kusa da Afrika ta yamma.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wannan yana da illa ga dakile yaduwar maleriya a Najeriya saboda ba a san nau'in sauron ba a yankin Afrika ta yamma ba."

Farfesa Salako ya kara da bayyana cewa, cibiyar binciken tana aiki da wasu kungiyoyi biyar domin samar da riga-kafin cutar a Najeriya, inda ya jaddada cewa masu bincike a Najeriya suna duba cigaban tun daga farko har karshe.

"Wannan yana da matukar amfani ta yadda idan aka samu sabuwar annoba ko cuta, sananniya ko ba sananniya ba, Najeriya za ta iya hada riga-kafin cutar da kanta," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel