Zafafan Hotunan Ummi Rahab Da Angonta Lilin Baba Suna Shan Soyayya

Zafafan Hotunan Ummi Rahab Da Angonta Lilin Baba Suna Shan Soyayya

  • Jarumar kannywood kuma amarya Ummi Rahab ta saki zafafan hotunanta tare da angonta Lilin Baba
  • Ummi ta kuma saki wasu zantuka da kalaman soyayya don jaddada irin kaunar da take yiwa mijin nata
  • Ta kuma yi masa addu’ar samun kariyar Allah yayin da yake ci gaba da bata kulawa da sanya farin cikinta sama da komai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Soyayya na kara karfi yayin da zama ke kara dadi tsakanin amarya kuma jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ummi Rahab da angonta kuma mawaki Shua’abu Lilin Baba.

Jarumar ta saki wasu zafafan hotunansu tare da mijin nata suna shan soyayya a shafinta na Instagram.

Ummi Rahab da Lilin Baba
Zafafan Hotunan Ummi Rahab Da Angonta Lilin Baba Suna Shan Soyayya Hoto: ummirahabofficial
Asali: Instagram

Sannan ta jaddada irin soyayyar da take yiwa mijin nata, tana mai alfahari da mallakarsa a matsayin abokin rayuwa.

Ta kuma bayyana cewa shine farin cikin zuciyarta tare da nuna jinjina a kan irin kulawar da yake mata.

Kara karanta wannan

Cin Amana: Ta Bi Shawarar Kawarta Ta Rabu Da Saurayinta Kan Cewa Ya Cika Girman Kai, Yanzu Kawar Na soyayya Da Shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga karin hotuna:

Ummi da Lilin Baba
Zafafan Hotunan Ummi Rahab Da Angonta Lilin Baba Suna Shan Soyayya Hoto: ummirahabofficial
Asali: Instagram

Ummi da Lilin Baba
Zafafan Hotunan Ummi Rahab Da Angonta Lilin Baba Suna Shan Soyayya Hoto: ummirahabofficial
Asali: Instagram

Ta rubuta a shafin nata:

“Kai ne dalilin farin cikina ❤️Yayin da kake kula da ni kana saka ni farin ciki Allah madaukakin sarki ya yi maka jagora sannan ya kare ka a duk inda kake❤️ ina kaunarka da dukka zuciyata ❤️na yi dacen samunka a matsayin mijina ❤️."

Bayan ta rubuta wadannan zantuka sun yiwa angon nata dadin inda ya je wajen yin sharhi ya zolaye ta da kodai ya kara sadaki ne.

Ya ce:

"Ko Dai In Kara Biyan Sadaki Ne?"

Jama'a sun yi martani

teema_yola ta rubuta:

"Masha Allahu"

minal__ahmad ta yi martani:

"Allah ya baku zaman lpy"

safiyyahbabashe ta ce:

"Gaskiyane sis masha Allah Ubangiji ya karo zaman lfy amin"

adam__nasir ya ce:

"Wai dama haka @lilin.baba yake da kyau"

sarah_saratoh_ ta rubuta:

"Mai daukarku photouna nan indai gwaro ne sai takaici ya kasheshi mashaallah tubarakallah allah yabaku zaman lafiya da zuri'a ta gari"

Kara karanta wannan

Duk Da Kudaden Da Nake Turowa Daga Turai, Matashiya Ta Koka Da Ganin Yanayin Danta A Bidiyo

Ta Bi Shawarar Kawarta Ta Rabu Da Saurayinta Kan Cewa Ya Cika Girman Kai, Yanzu Kawar Na soyayya Da Shi

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matashiyar ‘yan Najeriya mai suna Ugochi ta hadu da cin amana mafi muni bayan kawarta ta fara soyayya da saurayinta.

Tun farko dai kawar Ugochi din ita ta shawarceta da ta rabu da saurayin nata domin a cewarta ya cika takama da izza. Ita kuma sai ta bi shawarar wajen rabuwa da shi.

Ugochi ta je shafinta na Twitter don bayar da labarin wannan cin amana mafi girma da aka yi mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel