Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani Kan Bidiyon Barazanar Sace Buhari Da Yan Ta'adda Suka Fitar

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani Kan Bidiyon Barazanar Sace Buhari Da Yan Ta'adda Suka Fitar

  • Fadar shugaban Najeriya ta yi martani kan bidiyon da yan ta'addan jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja suka fitar a baya-bayan nan
  • A bidiyon, yan ta'addan da aka gani suna azabtar da mutanen da ke tsare a hannunsu sun yi barazanar tarwatsa Najeriya da kuma kama Shugaba Buhari da Gwamna El-Rufai
  • Garba Shehu, Kakakin Buhari ya ce shugaban kasar yana yi wa sojoji da jami'an tsaro dukkan abin da suke bukata don magance yan ta'addan kuma suna aiki nan bada dadewa ba za su magance yan ta'addan

Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi martani kan bidiyon da yan ta'adda suka fitar na barazanar cewa za su tarwatsa Najeriya, tana cewa jami'an tsaro ba su 'gaza ba kuma basira bata kare musu ba', rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mu muka tallata Buhari, dole mu fito mu fadi gaskiya, Naburaska ya cashe gwamnati

Yan ta'addan sun fitar da bidiyo inda suka yi barazanar cewa za su sace Shugaba Muhammadu Buhari.

Sojojin Najeriya.
Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani Kan Bidiyon Barazanar Sace Buhar Da Yan Ta'adda Suka Fitar. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da ya ke martani, babban hadimin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa shugaban kasa ya yi dukkan abin da ya dace ya yi a matsayinsa na babban kwamandan tsaro ta hanyar karfafa musu gwiwa, siyan kayan aiki da makamai kuma yana tsammanin sakamako mai kyau.

Sanarwar da kakakin shugaban kasar ya fitar ta ce "yan ta'addan na amfani da farfaganda ne da tada fitina don tilastawa gwamnati ta amince da bukatunsu na siyasa kuma hakan ba sabon abu bane a duk duniya.
"Jami'an tsaro da dakarun kasar ba su gajiya ba kuma basira bata kare musu ba. Suna da shirinsu da hanyoyin aikinsu wanda ba za su nuna ba a kafafen watsa labarai."

Kara karanta wannan

Dukan Fasinjojin Jirgin Kasa: Duk Munafukai Ne Masu Allah Wadai A Soshiyal Midiya, Naziru Sarkin Waka

"Matsalolin da ake fuskanta kan yan ta'addan jirgin kasan yana da yawa: Mataki irin yin ruwan wuta a dazukan inda suke zai biya bukatar masu ganin an dauki fansa amma me zai faru da wadanda aka sace? Ba su aikata laifi ba. Kawai sun shiga jirgi ne.
"Jami'an tsaro ba zaune suke ba. Sun san nauyin da ya rataya a kansu da abin da kasa ke tsammani daga gare su. Duk lokacin da za su yi wannan aikin suna fatan mutane su basu goyon baya.
"Ta'addanci matsala ne na duka duniya da ya dace kowa ya bada gudunmawa don yaki da shi - sojoji, farar hula da masu kamfanonin sadarwa. Wannan shine kadai hanyar da ake iya cin galaba kan yan ta'adda a kowanne bangare na duniya.
"Don taimaka wa kasa a halin da ake ciki, ya zama dole kafafen watsa labarai su kara bada tallafi su yaki amfani da kafar intanet da dandalin sada zumunta da yan ta'adda ke amfani da shi."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel