Ba zan biya ba: Bidiyon matashin da ya ki biyan kudi bayan budurwa ta kwaso kawaye 18 wurin cin abinci

Ba zan biya ba: Bidiyon matashin da ya ki biyan kudi bayan budurwa ta kwaso kawaye 18 wurin cin abinci

  • Wani bidiyo mai ban dariya wanda matashi ya ki biyan kudin abincin da budurwarsa da kawayenta suka lamushe a wurin cin abinci ya bayyana
  • Ranar zagayowar haihuwar budurwar ne, kuma a bayyane yake yadda saurayin ya fitar da budurwar amma sai ta kwaso kawayenta har su 18
  • Rikicin ya fara ne lokacin da suka kammala cin abincin kuma saurayin ya baje musu tsiya inda yace ba zai biya ko sisinsa ba

Wani matashi ya balle wa budurwarsa tsiya bayan ya ki biyan kudin abincin da ta lamushe tare da kawayenta 18 a wani gidan cin abinci.

Ranar bikin zagayowar haihuwar budurwarsa ne, hakan yasa ya kira ta don su shakata, amma kwatsam sai budurwar ta bayyana tare da kawayenta har su 18.

Budurwa mai kawaye
Ba zan biya ba: Bidiyon matashin da ya ki biyan kudi bayan budurwa ta kwaso kawaye 18 wurin cin abinci. Hoto daga TikTok/@viccgotti
Asali: UGC

Ba kowa zan biyawa ba

Kamar yadda aka gani a bidiyon TikTok din, mutumin bai ce komai ba har sai da 'yan matan suka kammala cinye abincin tas.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga nan ne ya ki biyan kudin. Hakan kuwa ya kawo mummunan sabani tsakaninsa da budurwar yayin da yace ba za biya ba.

Budurwar ta jaddada cewa tunda ranara zagayowa haihuwata ne, dole ne ya biyawa kowa kudin abincinsa. Sai dai wasu sun ce anya ba bidiyon barkwanc bane?

Legit.ng ta kasa tantance wannan ikirarin ha lokacin rubuta wannan rahoton, amma bidiyon ya samu masu kallao sama da miliyoyi a TikTok.

Budurwa ta kai karar magidanci wurin matarsa bayan yayi mata karyar mutuwar matarsa

A wani labari na daban, Dani Bose, kyakyawar Baturiya ta fallasa wani mutum da suka kwashe shekaru 30 da matarsa da aure amma yake neman matan banza a waje.

Budurwa mai shekaru 21 kuma tauraruwa TikTok ta bayyana yadda magidancin yayi ikirarin cewa matarsa ta mutu kuma yake son su hadu domin lalata.

Kara karanta wannan

Ganin Ta da Nayi Babu kaya Ya sa Nayi Mata Fyade Inji Matshi Da aka Kama Da Mahaukaciya

A bidiyon, ta bayyana yadda matarsa ta neme ta kuma tace tana son ta gwada mata cewa ko mijinta da suka yi shekaru 30 suna tare yana cin amanarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel