An Kama Wani Matashi Yana Lalata da Mahaukaciya A Suleja

An Kama Wani Matashi Yana Lalata da Mahaukaciya A Suleja

  • Dubun wani matashi mai shekara 21 ta cika, bayan da aka kama shi yana lalata da wata mahaukaciya a Suleja
  • Matashin da aka kama yana lalata da mahaukaciya yace yanayin da ya ganta babu kaya a jikinta ne ya ja hankalinsa zuwa wurin ta
  • Faifon bidiyo ya nuna yadda matashi ke kokarin yiwa mahaukaciyar fyade, kafin ta nemi taimako daga wajen mutane suka kawo mata dauki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Neja - Asirin wani matashi mai shekaru 21 ya tonu yayin da aka kama shi yana lalata da wata mahaukaciya a Unguwan Gwari da ke Karamar Hukumar Suleja, Jihar Neja. Rahoton Aminiya Dailytrust

RAPER
An Kama Wani Matashi Yana Lalata da Mahaukaciya A Suleja FOTO Legit.NG

Wakilin Daily Trust ya samu faifon bidiyon da ya nuna yadda matashin ke kokarin yiwa mahaukaciyar fyade, kafin ta nemi taimako daga wajen mutane suka kawo mata dauki.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari na duba yuwuwar haramta Okada a Najeriya

Matashin da jami’ain ’yan sanda sun yi awon gaba da shi an same shi da kullin tabar wiwi , ya dora alhakin faruwar lamarin ga shaye-shaye da kuma tsinuwa da mutanen kauyensu suka masa.

Ya ce yanayin da ya ga mahaukaciyar babu kaya a jikinta ne ya ja hankalinsa zuwa ga aikata lafin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matshin ya ce,

“Ba don jami’an tsaro ba, da watakila na yi lalata da ita ban san abin da ya zo mini ba, don Allah yafe ni, shekaruna 21 kacal.
“Akwai abubuwa da yawa a raina, matsalolina na da yawan gaske, ba ni da wanda zai taimake ni.

Bantaba sanin ina da ciki ba: Budurwa mai shafaffen ciki ta haihu a bandaki

A wani labari kuma, Wata mata mai shekaru 22 ta shiga matukar mamaki bayan ta haifa kyakyawa yarinya mace a yayin da ta shiga bandaki sakamakon ciwon cikin da bai kai ya kawo ba da ya kama ta.

Lucy Jones, mazauniyar Bristol dake Ingila, tace bata taba sanin tana dauke da juna biyu ba kuma tana tunanin tana ganin al'adarta ko a lokacin da ya kamata a ce tana dauke da cikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel