Hoton Sunan 'Allah' Da Wani Musulmi Ɗan Najeriya Ya Gani A Dafaffen Nama Da Ya Siya A Abuja
2 - tsawon mintuna
- Wani mutum dan Najeriya mai suna Wushishi Habibu mazaunin Abuja ya yi ikirarin ganin sunan Allah rubuce a jikin nama da ya siyo daga wurin cin abinci
- Wushishi ya bayyana cewa tsakaninsa da Allah bai taba yarda da irin labaran abubuwan ban mamaki irin wannan a baya ba amma gashi yanzu Allah ya nuna masa karara
- Ya ce ya tafi ya siyo abincin rana ne daga wani wurin cin abinci mai suna Abdullahi Aisha ya koma ofis ya bude zai fara cin nama kwatsam sai ga rubutun sunan Allah
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT Abuja - Wani dan Najeriya mazaunin birnin tarayya Abuja, Wushishi Habibu, ya yi ikirarin cewa ya ga sunan 'Allah' a rubuce a jikin nama da ya siya a wurin cin abinci a ranar Laraba 20 ga watan Yuli.
Ya rubuta:
"Tsakani na da Allah da ya hallice ni, yanzu na ga wannan a yayin da na ke cin abincin rana a ofis. Ban taba yarda da irin wannan da na gani a baya ba amma Allah ya nuna min shi karara a yau. Na siya abinci daga wurin cin abinci na Abdullahi Aisha kuma bayan na koma inci sai naga sunan Allah a rubuce a jiki. Allah da girma yake.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Martanin wasu yan Najeriya kan abin ban mamakin:
Gimbiyan Bosso:
"Allahu Akbar, alama ce ta karshen duniya. Allah ya fada cewa za mu rika ganin sunayensa a wuraren da ba mu yi tsammani ba. Allah ya mana jagora. Ammen."
Abdullahi Isiyaku ya ce:
"Ni ma shaida ne, zan iya tabbatarwa na gani."
Zainab Khalil Ismaila:
"Allah mai girma ne kuma zai cigaba da kasancewa mai girma."
Zainab Ibraheem cewa ta yi:
"Allahu Akbar, alamun karshen duniya, Allah ya yafe mana kurakurenmu."
Rabi Bello ta ce:
"Allah ya yafe mana kurakuren mu kuma ya bamu nasara da karshe mai kyau."
Rabiah Ahmad ta rubuta:
"Allahu Akbar na so da na zo mun ci naman tare".
Asali: Legit.ng
Tags: