"Yana Roko": Tsohon Shugaban ADC Ya Tona Wani Sirri kan Nafiu Bala
- Wanda ya kafa ADC, Ralph Nwosu, ya yi zargin cewa Nafiu Bala a baya yana neman N50,000 domin kuɗin motar zuwa tarukan jam’iyyar a Abuja
- Nwosu ya ce salon rayuwar Nafiu Bala ya sauya bayan ya shigar da ƙara kan rikicin shugabancin jam’iyyar a watan Satumban 2025
- Ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da hannu a rikicin cikin gida na ADC, yana ikirarin cewa tana ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Wanda ya kafa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), kuma tsohon shugaban jam’iyyar na farko, Ralph Nwosu, ya yi zarge-zarge kan Nafiu Bala.
Ralph Nwosu ya yi zargin cewa Nafiu Bala, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, a baya yana neman N50,000 domin kuɗin motar zuwa tarukan jam’iyyar a Abuja.

Source: Facebook
Nwosu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan rediyon Lagos Talks ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026, cewar rahoton jaridar TheCable.
Tsohon shugaban jam'iyyar ya yi zargin cewa salon rayuwar Bala ya sauya bayan ya shigar da ƙara kan rikicin shugabancin ADC a watan Satumban 2025.
Ya ce bayan shigar da ƙarar, Nafiu Bala ya fara zama a wani babban otel mai tsada, yana yawo da jami’an tsaro tare da amfani da motoci masu sulke.
Zargin sauyin rayuwar Nafiu Bala
Nwosu ya ce Bala ya fara amfani da motoci kirar SUV masu sulke, waɗanda ya ce sun fi uku, tare da rakiyar jami’an tsaro.
A kalamansa:
“Wannan Nafiu Bala, ya je kotu a watan Satumba, alhali mun kammala tsarinmu a watan Yuli. Daga watan Satumban ne ya fara zama a ɗaya daga cikin manyan otel-otel, ya fara yawo da jami’an tsaro. Ya samu motoci kirar SUV masu sulke, sama da uku, yana zirga-zirga tare da jami’an tsaro.”
Lokacin da aka tambaye shi ko wataƙila Nafiu Bala ya sayi motocin ne saboda fargabar tsaron rayuwarsa, Nwosu ya amsa da cewa:

Kara karanta wannan
"Ku ce ni da Kwankwaso mun gaza"; Peter Obi ya dauki muhimmin alkawari ga 'yan Najeriya
“Eh, amma za ka iya sayen motar SUV da kuɗinta ya haura N500m? Da sauran abubuwa makamantan haka?”
Yadda Nafiu Bala ke rokon kudi
Ya ce kafin wannan lokaci, Nafiu Bala ba ya iya zuwa tarukan jam’iyyar a Abuja sai an tura masa kuɗin mota.
Nwosu ya bayyana cewa shi da sauran shugabannin jam’iyyar ne suke taimaka masa da kuɗin sufuri idan aka gayyace shi taro.
“A baya, idan na gayyaci Nafiu Bala taro a Abuja, ba zai iya zuwa ba sai na tura masa ko dai N50,000 domin ya hau mota zuwa taron. Haka kuma, ba zai koma gida ba sai mun tara kuɗin da za mu biya masa kuɗin dawowa.” In ji shi.
Nwosu ya zargi gwamnatin Tinubu
Wanda ya kafa ADC ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da sha’awar rikicin cikin gida na jam’iyyar, yana mai cewa rikicin shugabancin ya fara ne bayan Nafiu Bala ya garzaya kotu.
Nwosu ya yi ikirarin cewa suna da faifan sauti da ke nuna shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa yana umartar wasu mutane da su ci gaba da zama a ADC domin su lalata jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro

Source: Facebook
Batun murabus din Nafiu Bala
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da wata takardar murabus da ake zargin tsohon mataimakin shugaban ADC na ƙasa, Nafiu Bala, ya rubuta.
Kotun ta yanke cewa ba a tabbatar da sahihancin takardae ba, don haka ba za a iya amfani da ita a matsayin hujjar cewa Nafiu Bala ya yi murabus daga muƙaminsa a jam’iyyar ba.
Asali: Legit.ng
