Pantami Ya Shiga Gombe duk da Kona Tayoyi, Toshe Hanya da Kai Masa Hari
- Wasu matasa sun kona tayoyi tare da toshe hanya a Jekadafari da ke kusa da gidan su Gwamna Inuwa Yahaya, a wani yunƙuri na hana Farfesa Isa Ali Pantami shiga Gombe
- Duk da lamarin, tawagar tsohon Ministan sadarwa ta samu damar wucewa ta hanyar tare da ci gaba da jerin gwanon motocinta zuwa wurin babban gangamin siyasa
- An kuma kai hari kan wasu motocin da ke cikin tawagar, inda wasu matasa dauke da makamai suka fasa gilasan motoci, kafin jami’an tsaro su shawo kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya samu nasarar shiga birnin Gombe duk da wani yunƙuri da wasu matasa suka yi na hana shi shiga jihar a ranar Talata.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito bayan shekaru 5, kotu ta sallami wanda ake zargi da kashe matarsa a Kano
Matasa sun banka wa tayoyi wuta tare da toshe hanyar Jekadafari, kusa da gidan iyalan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, a lokacin da Pantami ke shigowa birnin domin halartar wani babban gangamin siyasa da ya samu halartar dimbin jama’a.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa an shirya taron maraba da Pantami da gangamin ne ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar PDP a jihar Gombe, domin karrama shi bayan bayyana sunansa a cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamna.
Yadda matasa suka kona tayoyi
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wasu matasa ne suka kutsa kan babbar hanyar Jekadafari, inda suka tare ta da tayoyi kafin su banka musu wuta.
Hayakin baƙin da wutar ta fitar ya rufe sararin samaniya, lamarin da ya jefa direbobi, fasinjoji da mazauna yankin cikin fargaba.
An samu tsaiko a zirga-zirgar ababen hawa na wasu mintuna, inda direbobi suka dakatar da tafiyarsu ko kuma suka nemi wasu hanyoyin da za su bi domin isa inda suka dosa.
Haka kuma, wasu ’yan kasuwa da masu shaguna a yankin sun rufe wuraren kasuwancinsu cikin gaggawa saboda fargabar barkewar rikici tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa.
Tawagar Pantami ta wuce

Kara karanta wannan
Matsaloli 10 da Sheikh Isa Pantami ya tsallake wajen zama ‘dan takarar gwamna a Gombe
Duk da toshe hanyar da kuma wutar da aka kunna, ayarin motocin Pantami da ya ƙunshi daruruwan motoci ya samu damar wucewa ta wurin tare da ci gaba da tafiya zuwa inda aka shirya babban gangamin.
Magoya bayansa da ke cikin ayarin motocin sun ci gaba da rera wakokin goyon baya tare da sowa yayin da suke wucewa ta cikin hayakin tayoyin da ke ci.
Sai dai rahoton ya bayyana cewa wani rukuni na matasa dauke da makamai masu haɗari sun kai hari kan motocin da ke cikin ayarin, inda suka fasa gilasan motocin da dama.
Jami’an tsaro sun shiga lamarin
Sai dai jami’an tsaro da aka tura wurin sun gaggauta shiga tsakani domin shawo kan lamarin, kashe wutar da kuma cire abubuwan da aka yi amfani da su wajen toshe hanya.
Wani mazaunin yankin mai suna Sani Balarabe ya bayyana cewa lamarin ya ba su tsoro, domin ba su san abin da zai biyo baya ba bayan ganin matasan sun tare hanya.

Source: Facebook
Ya ce suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum ne kawai kafin kwatsam suka ga matasan sun mamaye hanyar tare da banka wa tayoyi wuta.
Alkawuran da Pantami ya yi
A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi alƙawarin yaƙi da talauci da samar da ayyuka.
Pantami ya bayyana waɗannan alƙawura ne a ranar Laraba, jim kaɗan bayan karɓar tutar takarar gwamna daga hannun shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Abdurrahman Muhammad.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga walwalar al’ummar jihar, musamman samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.
Asali: Legit.ng
