Ban dai ji dadi ba: Buhari ya yi Allah wadai da samun labarin kashe malamin Kirista a Kaduna

Ban dai ji dadi ba: Buhari ya yi Allah wadai da samun labarin kashe malamin Kirista a Kaduna

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da samun labarin kashe wani babban malamin addinin kirista
  • An sace wani malamin addinin kirista a Kaduna, daga bisani aka samu labarin kashe shi a cikin makon nan
  • Ana ci gaba da sace mutane tare da tada hargitsi a yankuna daban-daban a kasar nan tun farin mulkin Buhari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wani limamin cocin Katolika, Rabaran Fr. John Cheitnum na cocin Katolika da ke Kafanchan, kwanaki hudu bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi.

Ya mayar da martani kan lamarin ne a Abuja a ranar Laraba, Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, rahoron Vanguard.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi

Buhari ya yi ta'azziyar mutuwar faston kacolika
Ban dai ji dadi ba: Buhari ya yi Allah wadai da samun labarin kashe malamin Kirista a Kaduna | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewarsa:

"Na damu matuka da kisan da aka yi wa wannan babban malamin addini da wasu tsagerun mutane suka yi, wadanda da alama sun himmatu wajen haifar da hargitsi da tashin hankali a kasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Harin da ‘yan bindiga ke ci gaba da kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da masu riko da addini, babban abin damuwa ne ga wannan gwamnati, domin tsaro na daya daga cikin manyan al’amuran da muka alkawarta a yakin neman zabenmu.
“Ina mai sake tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa wannan kudurin nawa yana nan daram kamar da farko. Na mai dashi jiki a ko yaushe na kira zama da shugabannin tsaro akai-akai domin tattauna wadannan kalubale da kuma hanyar da za a bi a magance su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun sace wani babban Basarake a arewa

"Ba zan barin shugabannin jami’an tsaro su huta ba har sai mun sami mafita mai inganci ga wannan matsalar tsaro da ta dame mu.
"Tsaron dukkan ‘yan Najeriya shi ne babban abin da na sa a gaba, kuma ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa mun kuduri aniyar murkushe wadannan makiya bil’adama da duk wani abu da muke da shi.”

Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da shugabannin kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihar Kaduna bisa rasuwar Rev. Fr. Cheitnum, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

Wani shugaban APC ya yi ta maza, ya tsere daga hannun 'yan bindiga

A wani labarin, shugaban jam’iyyar APC gunduma ta 9 a karamar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo, Mista Godwin Aigbogun, ya kubuta daga maboyar wadanda suka sace shi.

Masu garkuwa da mutanen da ake zargin Fulani makiyaya ne, an ce sun bukaci iyalansa da su biya Naira miliyan 5, bayan da aka yi garkuwa da shi a hanyarsa ta komawa kauyensu daga gonarsa da ke Ologbo-nugu a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya fusata, ya yi kakkausan lafazi kan yajin aikin ASUU

Sakataren Yada Labarai na Jihar Barista Peter Uwadiae, ya tabbatar wa da jaridar Punch cewa jigon ya tsere ne da safiyar Laraba kuma ya ce tuni ya koma ga iyalansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel