Budurwa ta yi wuff da mahaifin saurayinta mai shekaru 89 bayan gano ya ci amanarta

Budurwa ta yi wuff da mahaifin saurayinta mai shekaru 89 bayan gano ya ci amanarta

  • Wata budurwa ta haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan da ta bayyana hotunanta tare da mahaifin saurayinta
  • An ce budurwar mai shekaru 23 ta dauki matakin mai ban mamaki ne bayan da ta kama saurayin nata da wata
  • Ta hanyar auren mutumin mai shekaru 89, dangantakarta da tsohon saurayin nata ya sauya daga saurayi da budurwa zuwa da matar uba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata budurwa ta auri mahaifin saurayinta mai shekaru 89 bayan da aka ce ta kama shi yana kulla alaka da wata ba ita ba.

Hoton budurwar mai shekaru 23 da mijinta tsofai-tsofai ya yadu a wani shafin Instagram mai suna The Savoy Show.

Yadda budurwa ta auri mahaifin saurayinta
Cin amana ko fansa: Budurwa ta yi wuff da mahaifinsa saurayinta mai shekaru 89 | Hoto: @thesavoyshow
Asali: UGC

Da take mayar da martani ga cece-kucen jama'a da ke mamakin aikinta, budurwar ta caccaki mutanen da ke kiranta da munanan sunaye.

A cikin wani faifan bidiyo da kafar yada labaran ta wallafa, ta yi magana kan yadda saurayinta ya yaudare ta tare da neman mata daban-daban ciki har da kawayenta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari na duba yuwuwar haramta Okada a Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ga dai abin da ta fadi:

“Don haka ake ta kirana da sunaye don na auri mahaifin tsohon saurayina, amma tsohon saurayina da ya yaudare ne ya nemi mata daban-daban ciki har da kawaye ba a kira shi da sunaye ba."

Kalli bidiyon:

Ra'ayoyin 'yan soshiyal midiya

@stephenp12 ya ce:

"Abin ban mamaki ne!!!!! yanzu za ta zama kaka tana lura dan rikonta wanda a zahiri a baya tsohon saurayinta ne..."

@jay_west.42 ya ce:

"Don kawai ya aikata abin da ya yi, ba yana nufin abin da kika yi daidai ba ne! Me ya sa mata suke kokari su daidaida halayensu ta hanyar kwatanta kansu da mazan da suka ce sun fi?!"

@lashaunhaywood said:

"Yana da shekaru 89 da dala miliyan 90 wannan shi ne dalilin da ya sa amma kaji bana jin haushin ta fa."

Kara karanta wannan

Yara sun fi dadin sha'ani: Hotunan soyayyar wata budurwa da dan shekara 18

@tiptoez ya ce:

"Ya yaudari mata da yawa, wasu daga cikinsu "abokai na ne" akwai alamar tambaya."

Hotunan soyayyar wata budurwa da matashi dan shekara 18 sun girgiza intanet

A wani labarin, yayin da mutane da yawa ke ganin ya dace mata su gina alaka da maza masu shekaru, wata 'yar Najeriya ta zo da sabon salo a irin nata ra'ayin.

Budurwar ‘yar Najeriyar mai shekaru 20 kwanan nan ta tafi shafin TikTok don nuna alfahari da saurayin ta mai shekaru 18 kuma ta sa mutane da yawa suna ta magana a kai.

'Yar Najeriyar mai shekaru 20 ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan ta nuna saurayinta a cikin wani bidiyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel