Da Ɗumi-Ɗumi: Jarumar Fina-finai ta yanke jiki ta faɗi, ta rasu kafin zuwa Asibiti

Da Ɗumi-Ɗumi: Jarumar Fina-finai ta yanke jiki ta faɗi, ta rasu kafin zuwa Asibiti

  • Fitacciyar jaruma a masana'antar Nollywood, Ada Ameh, ta mutu jim kaɗan bayan ta yanke jiki ta faɗi ba zato a jihar Delta
  • Ameh, wacce ta ce ga garinku nan a kan hanyar zuwa Asibiti, ta yi fice a shiri mai dogon zango 'The Johnson' a zamanin rayuwarta
  • An haife ta ranar 15 ga watan Mayu, 1974, kuma tauraruwarta ta fara haskawa a wani shiri a shekarar 1996

Delta - Shahararriyar Jarumar shirin fina-finai a masana'antar Nollywood da ke kudancin Najeriya, Adah Ameh, ta mutu, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Rahoto ya nuna cewa jarumar, wacce ta yi fice a shiri mai dogon zango, "The Johnson" ta rasu ne a Warri, jihar Delta ranar Lahadi da misalin ƙarfe 11:00 na dare.

Kara karanta wannan

Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara

Ada Ameh.
Da Ɗumi-Ɗumi: Jarumar Fina-finai ta yanke jiki ta faɗi, ta rasu kafin zuwa Asibiti Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta, ta bayyana cewa Ameh ta baƙunci wani babban Kamfanin Mai domin yin wani aiki lokacin da ta yanke jiki ta faɗi babu zato babu tsammani.

Nan take aka yi gaggawar kai ta Asibitin kamfanin NNPC na ƙasa amma ta ce ga garin ku nan a kan hanya tun kafin a ƙarasa harabar Asibiti, a cewar majiyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ƙara da cewa da yawan jaruman Fim abokanan aikinta sun yi tururuwar zuwa wurin da safiyar Litinin domin yin tozali da gawarta.

Yadda ta shahara a Nollywood

Marigayya Jaruma Ameh, wacce ta taka muhimmiyar rawa a matsayin Anita cikin shirin ‘Domitilla’ a shekarar 1996, ta shahara wajen fitowa a mai ban dariya, musamman a shiri mai dogon zango, ‘The Johnsons’.

An haifi marigayya Ada Ameh ranar 15 ga watan Mayu a shekarar 1974 a yankin Ajegunle, jihar Legas, kudu maso yammacin Najeriya, kamar yadda Vanguard ta tabbatar a rahotonta.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugabar matan jam'iyyar APC ta rasu bayan fama da rashin lafiya

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa jarumar ta sanya Bidiyonta da iyalanta suna cin abinci a shafinta na Instagram da misalin ƙarfe 12:53 na rana ranar Lahadi kafin mutuwa ta yi kira da daren ranar.

A wani labarin kuma kun ji yadda wani 'Ɗan PDP ya bindige kansa yayin murnar nasarar jam'iyyarsa a zaɓen Osun

Yayin da yake nuna jin daɗinsa da nasarar PDP, wani mutumi ya harbi kansa da bindiga a Ile-Ife ranar Lahadi.

Bayanai sun nuna cewa an garzaya da shi wani Asibiti mafi kusa kafin daga bisani a maida shi Asibitin koyarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel