Rundunar soji ta tsare jami’anta dake bakin aiki a lokacin harin gidan yarin Kuje

Rundunar soji ta tsare jami’anta dake bakin aiki a lokacin harin gidan yarin Kuje

  • Hukumar soji Najeriya ta tsare jami'anta dake bakin aiki a lokacin da yan ta'adda suka kai wa gidan yarin kuje hari
  • Sojin Najeriya na fuskantar matsin lamba wajen al’umma akan janye sojojin da ke gadin kurkukun kuje sa'o'i 24 kafin harin
  • Masu bincike sun sun yi zargin samu masu zagon kasa a cikin rundunar jami’an tsaro Najeriya dake kawo cikas a harkar tsaro

Abuja - Ana ci gaba da gudanar da bincike kan harin ta'addancin da aka kai a cibiyar tsaro ta Kuje a daidai lokacin da rundunar sojojin Najeriya ta tsare sojojin da ke bakin aiki a wannan ranar domin amsa tambayoyi. Rahoton LEADERSHIP

Legit.NG ta rawaito yadda ‘yan ta’adda suka kutsa cikin gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar 5 ga watan Yuli inda suka sako daruruwan fursunoni ciki har da ‘yan Boko Haram 64.

Kara karanta wannan

Fashin magarƙama: An kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje ɗauke da kayan laifi a Katsina

Sojoji da jami’an leken asiri da hukumar gyaran fuska ta Najeriya suna fuskantar matsin lamba saboda gazawar su wajen dakile hari ko kuma fatattakar ‘yan ta’addan a lokacin da suka kawo harin.

A binciken da LEADERSHIP Weekend ta yi, ya nuna cewa a halin yanzu jami’an sojin da ake tsare da su suna fuskantar tambayoyi daga kwamitin bincike na sojoji.

Prison
Rundunar soji ta tsare jami’anta dake bakin aiki a lokacin harin gidan yarin Kuje FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumomin soji na fuskantar suka wajen al’umma akan janye sojojin da ke gadin kurkukun sa'o'i 24 kafin harin.

Masu lura da al’amura sun sun yi zargi akwai masu zagon kasa a cikin jami’an tsaro kuma sun yi kira da a gudanar da bincike.

Wakilin LEADERSHIP ya samu labarin cewa jami’an tsaron da ke bakin aiki a wannan rana ba su yi wani turjiya ba a lokacin da ‘yan ta’addan suka far wa gidan yarin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya fusata, ya yi kakkausan lafazi kan yajin aikin ASUU

Kuma harsashen da aka samu a harabar gidan yarin su ne wadanda maharan suka harba wato sojoji ‘yan sanda, DSS, Civil Defence da masu gadin gidan yari dauke da makamai ba su mayar da martini ba.

'Yan Bindiga Da yan ta'adan Ansaru sun fafata a jihar Kaduna

A wani labarin kuma, Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ‘yan kungiyar ta’addar Ansaru hari a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna. Rahoton Daily Trust

Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan kungiyar suna yin wa’azi ga jama’ar yankin ne a lokacin da ‘yan bindiga suka bude wuta, inda suka kashe yan kauyen biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel