Bidiyo: Daga zuwa yawon sallah, ta dawo ta tarar da gidanta tare da motarta kurmus
- Wata mata da ta zamoabun tausayi ta wallafa bidiyon yadda gidanta yayi kurmus bayan ta fita yawon sallaha da kawayenta
- An gano yadda gidan ya kama da wuta kuma makwantanta suka dnga kokarin kashewa, amma sai da ta cinye gidan da motarta dake harabar gidan
- Ta saki bidiyon lokacin da take dumuzgu da naman rago amma tace a lokacin bata san bakin ciki ne zai biyo baya ba idan ta koma gida
Wata mata da ta bar gidanta domin shagalin sallah da kawaye ta dawo ta tarar da gidanta na ci da wuta har da motar hawanta.
Ta wallafa bidiyon kanta tana cin naman sallah kuma ta sanar da cewa a lokacin bata san yadda ranar zata kasance mata ba.
A farkon bidiyon da ta wallafa, ta nuna yadda take shagalinta da naman rago, amma a karshe sai ta sako yadda wuta ta kone gidanta da motarta.
2023: Saura kwana uku a rufe, jam'iyyun su Kwankwaso da Sawore ba su kai sunayen yan takararsu na jihohi ba, INEC
Mazauna yankin sun yi kokarin ganin sun kashe wutar amma sun kasa ceto ginin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dukkan gidan da kadarorinta sun kone kurmus. Motar matar da aka ajiye a farfajiyar gidan itama ta lalace a wutar da ta tashi, LIB ta ruwaito.
Ta kara da bayyanawa a bidiyon cewa, dole yanzu ta fara neman inda zata sanya kanta tayi bacci. Ga bidiyon a kasa:
Bayan kama matar aure dumu-dumu da gardi, an tilasta mata zagaya kauye da mijinta a kafadarta
A wani labari na daban, an tirsasa wata matar aure ta dauka mijinta a kafadunta kuma ta zagaye titunan kauyensu bayan an kama ta dumu-dumu da wani gardi.
Shafin LIB ya ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Borpadaw aake Indiya a ranar 3 ga watan Yulin 2022.
Matar tayi batan-dabo na tsawon sati kuma mijinta da sirikanta sun dinga nemanta amma basu ganta ba.
Daga bisani sai mijin ya yanke shawarar mika rahoton batan matarsa kuma a lokacin ne wani yazo ya sanar da jami'ai cewa ta tare ne a gidan saurayinta.
Asali: Legit.ng