Rigima Sabuwa: NDC Ta Bankado Makarkashiyar da APC Kulla Wa 'Yan Takararta

Rigima Sabuwa: NDC Ta Bankado Makarkashiyar da APC Kulla Wa 'Yan Takararta

  • Jam’iyyar NDC ta zargi APC da amfani da kuɗi, muƙaman siyasa da sauran abubuwan more rayuwa wajen jawo wasu ’yan takararta su sauya sheƙa
  • NDC ta ce za ta gudanar da sababbin zaɓukan cikin gida domin zaɓen ’yan takarar da za su maye gurbin waɗanda suka fice daga jam’iyyar
  • Zargin ya biyo bayan murabus ɗin Ibrahim Kashim, ɗan takarar gwamnan Bauchi na NDC, da kuma sauya sheƙar Sanata Rufai Hanga zuwa APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki kan sauya shekar wasu 'yan takararta.

NDC ta zargi APC da bayar da kuɗi, muƙaman siyasa da sauran abubuwan ƙarfafawa domin jawo wasu daga cikin ’yan takararta su sauya sheƙa zuwa APC.

NDC ta yi zarge-zarge kan APC
Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson Hoto: @IamHSDickson
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da Osa Director, mai magana da yawun NDC na ƙasa, ya fitar ranar Talata, 20 ga watan Oktoban 2027 a shafin X.

Kara karanta wannan

Sanata Tambuwal na shirin ficewa daga ADC zuwa APC? An ji yadda zancen yake

Jam’iyyar ta ce tana sane da abin da ta kira yunƙurin APC na shawo kan wasu ’yan takararta su fice daga cikinta.

NDC ta zargi APC da ƙoƙarin jawo ’yan takararta

Sanarwar ta ce:

“NDC tana sane da dabarun APC na neman cimma burinta ta kowace hanya, inda ta koma bayar da kuɗi, muƙaman siyasa da sauran abubuwan amfani domin jawo wasu ’yan takarar jam’iyyarmu masu son kuɗi su sauya sheƙa zuwa jam’iyyar da ke durƙushewa.”

NDC ta ce ba ta damu da waɗanda suka fice daga cikinta ba, tana mai cewa mutanen ba su da ƙimomi da akidun siyasa da jam’iyyar ta tsaya a kai.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"Ga waɗanda suka faɗa tarkon nan, a bayyane yake cewa ba su da ƙimomi, kyawawan halaye da cikakken goyon baya ga akidar siyasar da jam’iyyarmu mai girma ta yi imani da ita. Ba su taɓa kasancewa cikakken ɓangare na mu ba.”

Kara karanta wannan

2027: PDP, NDC sun shiga kafar wando da INEC kan cire sunayen yan takararsu

Jam’iyyar ta ce tana yi wa waɗanda suka fice fatan alheri a tafiyarsu ta siyasa, duk da cewa ta bayyana matakin nasu a matsayin abin da ba za ta yi nadama a kansa ba.

NDC za ta zaɓi sababbin ’yan takara

Director ya ce NDC za ta gudanar da sababbin zaɓukan cikin gida domin zaɓen ’yan takarar da za su maye gurbin waɗanda suka fice a mazabun da abin ya shafa.

Ya ce matakin zai yi daidai da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta shekarar 2026. Ya kuma buƙaci mambobi da magoya bayan jam’iyyar kada su damu da sauya shekar, yana zargin APC da ƙoƙarin raunana NDC ta hanyar jawo wasu daga cikin ’ya’yanta su bar ta.

Ɗan takarar gwamnan Bauchi ya yi murabus

Duk da cewa mai magana da yawun NDC bai ambaci sunayen waɗanda suka sauya sheƙa kwanan nan ba, sanarwar ta zo ne kusan sa’o’i 24 bayan Ibrahim Kashim, ɗan takarar gwamnan Bauchi na jam’iyyar, ya sanar da murabus ɗinsa.

A cikin wasiƙar da ya aikewa shugaban NDC na ƙaramar hukumar Bauchi, mai kwanan wata 16 ga Oktoba, 2026, Kashim ya ce ya yanke shawarar ne bayan yin nazari sosai.

Kara karanta wannan

El Rufai ya san matsayarsa da kotu ta yanke hujunci kan karar da ya shigar da DSS

Kashim bai bayyana matakin da zai ɗauka na gaba ba. Sai dai rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar ya koma APC a makonni masu zuwa.

Sanata Rufai Hanga ya koma APC

A ranar 3 ga Agusta, Rufai Hanga, sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya kuma tilo daga Arewa a majalisar dattawa a ƙarƙashin NDC, shi ma ya yi murabus daga jam’iyyar.

Daga bisani, ya koma APC a hukumance ranar 6 ga Satumba. Hanga ya sanar da murabus ɗinsa ne ta wasiƙar da ya aikewa shugaban jam’iyyar na mazabar Najeria, da ke ƙaramar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

Wasu ’yan takara sun sauya sheƙa zuwa APC

Haka kuma, kwanaki kaɗan da suka gabata, an samu rahotannin cewa wasu ’yan takarar majalisar wakilai da na majalisun dokokin jihohi daga jam’iyyun African Democratic Congress (ADC) da NDC a jihohin Taraba, Jigawa, Kaduna, Kano da Plateau sun sauya sheƙa zuwa APC.

Sai dai sanarwar NDC ba ta ambaci sunayen waɗannan ’yan takara ko kuma takamaiman matakan da APC ta ɗauka wajen shawo kansu ba.

NDC ta zargi APC da shirya makarkashiya
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu jiga-jigan jam'iyyar NDC Hoto: @IamHSDickson
Source: Facebook

'Yan takarar NDC sun yi zargi kan Kwankwasiyya

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An maka INEC kara gaban kotu kan N126bn

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ’yan takarar Majalisar tarayya biyar na NDC a jihar Kano sun yi zarge-zarge kan Kwankwasiyya.

'Yan takarar sun zargi tafiyar Kwankwasiyya da tsoratar da su kan waɗanda ya kamata su wakilci jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng