Hotuna da Bidiyo: Dandazon jama'a sun fito nuna wa Buhari kauna yayin da yake takawa zuwa gida daga idi

Hotuna da Bidiyo: Dandazon jama'a sun fito nuna wa Buhari kauna yayin da yake takawa zuwa gida daga idi

  • Dandazon masoyan shugaban kasan Muhammadu Buhari a garin Daura na jihar Katsina sun fito suna kwarara masa addu'o'i da kalaman yabo
  • Bayan idar da sallar idin babbar sallah da yayi a masallacin idin Kofar Arewa, shugaban kasan ya tattaka a kafa har zuwa gidansa
  • A bidiyon da hadiminsa, Buhari sallau ya wallafa a Instagram, an gan shi yana dagawa jama'a hannu yayin da suke nuna masa kauna a bayyane

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya tattakawa a kasa daga filin sallar Idi a Daura jihar Katsina zuwa gidansa domin taya jama'a murnar babbar sallah.

Baba shakka wannan cigaban ya birge dandazon masoyan shugaban kasan inda suka dinga ihu, addu'o'i tare da yabo ga shugaban kasan.

Kara karanta wannan

Kyawawan Hotunan Buhari da Yusuf a Filin Sallar Idin Babbar Sallah Sun Kayatar

Baba a Daura
Hotuna da Bidiyo: Dandazon jama'a sun fito nuna wa Buhari kauna yayin da yake takawa zuwa gida daga idi. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Hadimin shugaban kasan, Buhari sallau ne ya wallafa kyawawan hotunan tare da bidiyon a Instagram kan yadda dubban jama'ar suka fito nuna soyayyarsu ga shugaban kasan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baba a Daura
Hotuna da Bidiyo: Dandazon jama'a sun fito nuna wa Buhari kauna yayin da yake takawa zuwa gida daga idi. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

AGF Malami yayi wuff da diyar shugaba Buhari, hotuna suna bayyana

A wani labari na daban, A ranar 8 ga watan Yulin 2022 ne aka daura auren Nana Hadiza Muhammadu Buhari da AGF Abubakar Malami, SAN.

An daura auren a Abuja yayin da aka yi karamin biki a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake Abuja tare da 'yan uwa da abokan arziki.

Daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya tabbatar da hakan.

"Eh, da gaske ne, antoni janar na tarayya ya aura diyar shugaban kasa."

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ba zam huta ba har sai na samar da sassauci ga yan Najeriya, Shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel